Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Za A Yi Babban Zaɓen 2023 Ranar 18 Ga Fabrairu – INEC

by
1 year ago
in LABARAI, RIGAR 'YANCI
2 min read
Hukumar Zabe
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Agaji Ta Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 131 Ga Marayu A Kebbi

Nijeriya Na Bukatar Shugaban Da Kasar Ce Kawai A Gabansa —Obasanjo

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 18 ga Fabrairu ne za a gudanar da Babban Zaɓen shekarar 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba a cikin jawabin da ya gabatar wajen taron dandalin sauraron jama’a a kan Ƙudirin ƙirƙiro Dokar kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe ta Ƙasa wanda Kwamitin Hukumar Zaɓe na Majalisar Dattawa ya shirya a Abuja.
Farfesa Yakubu ya ce: “Wannan Hukuma ta ƙosa ta san irin dokar da za ta yi aiki da ita wajen aiwatar da manyan zaɓuɓɓukan shekarar 2023. A bisa ƙa’idojin da Hukumar ta kafa, za a gudanar da manyan zaɓuɓɓukan 2023 ne a ranar Asabar, 18 ga Fabrairu, 2023, wanda ya kama shekara ɗaya da wata tara da mako biyu da kwana shida daidai daga yau ɗin nan ko kwanaki 660.”
Shugaban ya ce shekaru 13 bayan shawarar da Mai Shari’a Muhammadu Lawal Uwais ya bayar kan a kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe (National Electoral Offences Commission), da kuma wasu rahotannin kwamitoci daban-daban a kan batun, “a yau ga mu a wajen wannan taro na tarihi domin mu bada namu shawarwarin kan wannan doka.”
Ya ce, “Ba shakka, an ɗora wa INEC ayyuka masu yawa domin ana yin zaɓuɓɓuka a sassan Nijeriya a duk tsawon shekara.
“Tun daga zaɓen 2015, an gudanar da shari’u 124 kan laifuffukan zaɓe amma a guda 60 kaɗai ne aka yanke hukunci.”
Ya ƙara da cewa: “To amma, a yayin da mu ke jin daɗi game da wannan taron na yau, mu na kuma so a fito da tsarin doka mai suna Dokar Zaɓe (Gyararriya) wanda a kan ta za a aiwatar da zaɓuɓɓukan 2023, wanda za a yi a ranar 28 ga Fabrairu, 2023, kuma a rattaba hannu a kan ta a kan lokaci.”
Tun da fari, sai da Shugaban Kwamitin Hukumar Zaɓe na Majalisar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, ya bada tabbaci ga dukkan masu ruwa da tsaki cewa Ƙudirin Dokar Zaɓe (Gyararriya) na 2021 ya na samun kulawa kuma ana fatan Shugaban Ƙasa zai rattaba hannu a kan ta.
Gaya ya ce ba shakka kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe ta Ƙasa “zai canza labarin tsarin mu na gudanar da zaɓe.”
Wanda ya kawo ƙudirin kafa Hukumar Hukunta Laifuffukan Zaɓe ta Ƙasa, Sanata Abubakar Kyari, ya ce an fara ƙudirin kafa hukumar ne tun a Majalisar Dattawa ta 8 lokacin da ya kawo shawarar ƙudirin tare da Ovie Omo-Agege saboda sun fahimci cewa INEC ba ta iya hukunta ko da kashi 1 cikin ɗari na laifuffukan zaɓe, saboda haka akwai buƙatar a ɗauke wannan aikin daga kafaɗun ta, a bar ta ta yi aikin ta da kyau.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Korona: Gwamnatin Kaduna Ta Umarci Ba’arin Ma’aikata Su Yi Aiki Daga Gida

Next Post

Tsaro: Gwamnatin Katsina Za Ta Hada Kai Da Tsofaffin ’Yan Sanda

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Agaji Ta Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 131 Ga Marayu A Kebbi

Kungiyar Agaji Ta Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 131 Ga Marayu A Kebbi

by Umar Faruk
11 hours ago
0

...

Nijeriya Na Bukatar Shugaban Da Kasar Ce Kawai A Gabansa —Obasanjo

Nijeriya Na Bukatar Shugaban Da Kasar Ce Kawai A Gabansa —Obasanjo

by
13 hours ago
0

...

Legas: Mazauna Yankin Lekki Na Zaman Dar-Dar Kan Yuwuwar Kai Masu Hari

Legas: Mazauna Yankin Lekki Na Zaman Dar-Dar Kan Yuwuwar Kai Masu Hari

by Abubakar Abba
14 hours ago
0

...

2023: Kwamishinonin Ganduje 7 Da Ya Amince Da Ajiye Aikinsu Da Ukun Da Ya Yi Watsi Da Su

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Daliban Kwaleji 4 A Kaduna Sun Bukaci Kudin Fansa

by Abubakar Abba
15 hours ago
0

...

Next Post
Gwamnatin Katsina

Tsaro: Gwamnatin Katsina Za Ta Hada Kai Da Tsofaffin ’Yan Sanda

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: