Za A Yi Da-na-sanin Ayyana ‘Yan Bindiga A Matsayin ‘Yan Ta’adda –Sheikh Gumi

Fitaccen malamin da ke da’awar yi wa ‘yan bindiga masu satar mutane wa’azi, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa za a yi da-na-sanin in har aka ayyana su a matsayin’ yan ta’adda. Malamin ya faɗi hakan ne a wata sanarwar da aka wallafa a shafinsa na Facebook.

Tuni dai ‘yan majalisar a Nijeriya suka nemi gwamnatin Tarayya ta ayyana ‘yan bindigar da suka addabi yankunan arewacin Nijeriya a matsayin ‘yan ta’adda. A cikin sanarwar, Sheikh Gumi ya yi gargadin cewa “Da zarar an ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje za su samu gindin zama. Ya kuma ce wannan zai iya janyo ra’ayin matasan da ke fama da rashin aikin yi.

Sai dai kuma a cikin bayanansa malamain ya ce ayyukan da ‘yan bindigar suke aikatawa sannu a hankali sunansa ta’addanci: “Saboda duk inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, ta’addanci ne tsantsarsa.”

Exit mobile version