Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Za A Yi Jana’izar Babban Basarake, Mai Tangale, Ranar Lahadi

by Muhammad
January 13, 2021
in LABARAI
3 min read
Tangale
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
  • Rasuwarsa Babban Rashi Ne Ga Jihar Gombe – Gwamna Inuwa

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya kafa kwamiti karkashin Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, da aka dora wa alhakin shirye-shiryen bikin jana’izar Marigayi Mai Tangale, Dakta Abdul Bubu Maisheru II, inda aka sanya ranar Lahadi mai zuwa, 16 ga Janairu, 20121, a matsayin ranar binne shi.

samndaads

Wakilinmu ya nakalto cewa, Abdu Buba dai shine Mai Tangale na 5 wanda ya rasu ne a ranar 10 ga watan Janairu, yana da shekara 72 a duniya bayan gajeren rashin lafiya da ta riske shi.

Sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya sanar da batun kafa kwamitin shirye-shiryen bison babban basaraken, inda ya ce ranar Lahadi 16 ga Janairu ne za ta kasance ranar bison marigayin basaraken.

Sauran sun hada da Justice Beatrice Iliya da kuma Justice Idi Appolos na babban kotun jihar, tare da Misis Margret Audu, shugabar karamar hukumar Billiri.

Saura sun kunshi, Hon. Mela Audu Nunghe (SAN), kwamishinan ayyukan musamman da takwaransa na ayyuka da gida Injiniya Abubakar Bappah Musa , Group Captain Bitrus P. Bilal (Rtd) mai baiwa gwamnan shawara kan tabbatar da bin dokoki, Mista Babaji Babadidi, shugaban SUBEB da Barr. Abdulrasheed Ajuji Waziri wanda shine (Wazirin Tangale) kuma kwamishian kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu, inda kuma Hon. Ibrahim Dasuki Jalo Waziri zai kasance matsayin sakataren kwamitin.

A wani labari makamancin wannan Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ziyarci fadar Mai Martaba Mai Tangale dake karamar Hukunar Billiri domin jajantawa bisa rasuwar babban Basaraken Mai Tangale Dakta Abdu Buba Maisheru II, inda ya shawarci iyalan marigayin basaraken da al’ummar kasar Tangale su kwantar da hankalin su, su ci gaba da dabbaka koyarwar zuman lafiya da marigayi Uban kasan ya koyar.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ziyarar, gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa Allah zai shigewa al’ummar Tangale gaba da gwamnatin Jihar Gombe wajen yin abin da ya dace anan gaba.

Ya ce, “Za mu ci gaba da hada kanmu a matsayin iyali guda ba tare da rarrabuwa ba, kuma Allah cikin hikimarsa zai mana jagora wajen yin abin da ya dace”.

A yayin ziyarar, Gwamna Inuwa ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar Parfesa Ibrahim Abubakar Njodi, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Alhaji Abubakar Inuwa Kari, da kwamishinoni da shugaban riko na Jam’iyyar APC Mr. Nitte Amangal, da mashawartan gwamna na musamman da sauran manyan jami’an gwamnati.

Tun farko a sakon ta’aziyya da gwamnan ya fitar, ya bayyana kaduwa bisa rasuwar Mai Martaban Dakta Abdu Buba Maisheru na 2, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba abun koyi, wanda za a ci gaba da tunawa da shi da irin sadaukarwar sa kan tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.

Gwamna Inuwa ya bayyana marigayi Mai Tangalen a matsayin Sarkin da ake mutuntwa da darajtawa, wanda ya kawo ci gaba, zaman lafiya da hadin kai a kasar Tangale da Jihar Gombe a shekaru 19 da ya shafe kan karaga.

Ya ce, “Mai Tangale ya ciri tuta ta hanyar sadaukar da kansa don tabbatar da dunkulalliyar al’ummar Tangale tsintsiya madaurinki daya, kasancewarsa mamba a majalisar sarakuna ta Jihar Gombe, kuma shugaban majalisar sarakuna Kiristoci na arewacin Nijeriya.

“Tabbas za mu yi rashi da kewar shawarwari da nusantarwa irin nasa na uba.”

Ya kuma yaba da kokarin uban kasan wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban zamanta kewa a kasar Tangale, lamarin da ya sa ya zamo abun kauna da girmamawa ga talakawansa dama duk wanda ya yi mu’amala da shi.

A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, Gwamna Inuwa ya na mika cikakkiyar ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da kasar Tangale bisa wannan babban rashi, yana mai addu’ar Allah ya baiwa al’ummar Tangale da na Jihar Gombe hakurin jure wannan babban rashi.

SendShareTweetShare
Previous Post

’Yan Sandan Kano Sun Bajekolin Barayi Da ’Yan Damfarar Waya

Next Post

Malaman Addini Sun Bukaci Kukah Ya Bar Sakkwato

RelatedPosts

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

Buba Marwa Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar NDLEA

by Muhammad
10 hours ago
0

Daga Abba Ibrahim Gwale, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince...

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Yau Za A Yi Karon Batta A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

by Sulaiman Ibrahim
20 hours ago
0

 Jam’iyyu 11 ne za su fafata PDP Kwankwasiyya ta ce,...

Sojoji

Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

by Sulaiman Ibrahim
20 hours ago
0

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci...

Next Post
Kukah

Malaman Addini Sun Bukaci Kukah Ya Bar Sakkwato

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version