Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta ce daga ranar Juma’a zuwa Lahadi za a yi ruwan sama mai yawa a wasu jihohi na ƙasar nan.
Jihohin da za a fi samun ruwan sama su ne: Kano, Katsina, Sakkwato,Kebbi, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Yobe da Taraba.
A waɗannan wurare ruwan zai zo da iska mai ƙarfi.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta ce za a samu ruwan sama kaɗan a jihohin Nasarawa, Benuwe, Kogi, Kwara, Neja, Filato da kuma Abuja.
A yankin Kudu kuma, za a samu ruwan sama kaɗan tare da yanayin zafi a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ondo, Edo, Enugu, Imo, Abiya, Anambra, Delta, Ribas, Bayelsa, Cross Ribas da kuma Akwa Ibom.
NiMet ta gargaɗi mutane su yi hattara a lokacin ruwan sama, musamman masu tuƙin mota, sannan a cire na’urorin lantarki daga wuta, kuma a guji zama ƙarƙashin manyan bishiyoyi.
Haka kuma, ta shawarci manoma su guji amfani da taki da maganin ƙwari kafin ruwa ya sauka.