Shugaban kwamitin hana yaduwar annobar cutar Korona na Jihar Kano, Tijjani Hussaini, ya bayyana cewa, gwamnati ta ware wasu asibitoci da suka kai 509 da za a rika yi wa al’umman Kano allurar rigakafin.
Hussaini ya bayyana cewa asibitin Dala, asibitin Aminu Kano da asibitin Muhammadu Abdullahi Wase na daga cikin asibitocin da gwamnati ta zaba domin aikin yin rigakafin Korona.
Hussaini ya kara da cewa gwamnati ta rarraba yadda za a yi wa mutane allurar rigakafin zuwa gida hudu.
A farko za a yi wa jami’an lafiya da jami’an tsaro, sune za a fara yi wa rigakafin. Daga nan kuma sai ma’aikatan lafiyan da basu yi allurar rigakafin ba a rukunin farko da tsofaffin da suka wuce shekaru 50 duk su ne, ‘yan rukunin na biyu.
A rukuni na uku kuma za a yi wa duk mutanen da suke fama da wasu cututtuka a jikin su wadanda ba Korona ba. Bugu da kari kuma daganan sai a yi wa sauran mutane allurar rigakafin a rukuni na hudu.