Nasir S Gwangwazo" />

Za A yi Zaɓen Gwamnan Anambara Ranar 6 Ga Nuwamba – INEC

Zaben Dan Majalisa

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 za a yi zaɓen gwamnan Jihar Anambara.

Hukumar ta bayyana jadawalin ranar zaɓen da abubuwan da za a aiwatar ne a cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Talata a Abuja.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, wanda ya bada sanarwar, ya ce hukumar ta yi wani zama a ranar Talata inda ta tattauna kan zaɓen na Anambara.
A cewar sa, za a yi zaɓuɓɓukan share fage tare da warware duk wani saɓani da ka iya tasowa a tsakanin ranar 10 ga Yuni zuwa ranar 1 ga Yuli.
Ya ce, “Kamar yadda Sashe na 178(1) da (2) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara shi) da Sashe na 25(7) da (8) na Dokar Zaɓe ta 2010 (kamar yadda aka gyara ta) su ka tanadar, ba za a gaza gudanar da zaɓen mukamin Gwamnan Jiha a cikin kwana 150 ƙasa da ko kuma kwana 30 sama da ƙarewar wa’adin mulkin wanda ya riƙe mukamin ba.
“A Kundin Tsarin Mulki da kuma Doka, wa’adin mulkin gwamnan Anambara zai ƙare ne a ranar 17 ga Maris, 2022, saboda haka rana mafi kusa da za a iya yin zaɓen na Gwamnan Anambara za ta kama 18 ga Oktoba, 2021 sannan ba za a zarce ranar 15 ga Fabrairu, 2022 ba don a yi zaɓen.
“A bisa ikon da Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe da sauran dokoki su ka ba ta a wannan lamari, INEC ta saka ranar 6 ga Nuwamba a matsayin ranar da za a yi zaɓen Gwamnan Anambara.”
Mista Okoye ya kara da cewa, “Don haka, yanzu hukumar ta fitar da jadawalin lokutan zaɓe da sauran ayyuka na zaɓen.
“Bisa ga wannan jadawalin lokutan zaɓe da ayyukan da su ka jiɓince shi, hukumar za ta fitar da sanarwar dokar gudanar da zaɓen a ranar 9 ga Yuni.
“Za a gudanar da karɓar fom mai lamba EC9 (wanda a da ake kira CF001) da fom mai lamba EC9B (wanda a da ake kira CF002) don shiga zaɓen a ranar 10 ga Yuni, sannan za a gudanar da zaɓuɓɓukan share fage da warware saɓanin da ka iya tasowa a tsakanin ranakun 10 ga Yuni da 1 ga Yuli.”

Exit mobile version