Abubakar Abba" />

Za A Zuba Biliyan N10.89 A Aikin Noma Na LIFE-ND 

Mataimakin shugaban NDDC Joi Nunieh ya ce shirin (LIFE-ND) na fannin aikin noma zai taimaka wajen inganta rayuwar mutanen Neja-Delta musamman wajen rage yawan hijira da mutane ke yi daga kauyuka zuwa birane.

Joi Nunieh ya sanar da hakan ne a hirarsa da manema labarai a garin Fatakwal, inda a cewar mataimakin hukumar, NDDC za ta bada gudunmuwar naira biliyan 10.89 don samu cin nasarar shirin (LIFE-ND).

Mataimakin shugaban na NDDC Joi Nunieh ya ce shirin na (LIFE-ND), Gwamnatin Tarayya ce ta kirkiro dashi kuma ta yi alkarin za ta kashe akalla naira biliyan 46.83 domin inganta aiyukan noma a jihohi tara na yankin Neja-Delta mai albarkar man fetur.

Ya sanar da cewa, Jihohin da za su amfana da shirin da ke a Kudu sun hadada, da ke ita Neja Delta, Abia, Akwa Ibom, Bayelsa, Koros Riba, Delta,Edo,Imo,Ondo da Ribas.

Ya cigaba da cewa, manufar shirin na aikin noma na (LIFE-ND) Gwamnati Tarayya ta tsara shine ne domin samar da abinci da inganta tattalin arzikin kasa da na wannan yanki, inda ya kara da cewa, gwamnati za ta yi amfani da wadannan kudaden wajen inganta kiwon kaji, kifi, noman kwakwar manja, rogo, shinkafa da ayaba.

Mataimakin shugaban NDDC Joi Nunieh ya ce shirin (LIFE-ND) ya kara da cewa, har ila yau, Gwambatin Tarayya za ta kuma yi kokarin kawar da matsalolin rashin kudin jari,rashin filin noma da rashin kasuwar amfanin gonan da aka noma a yankin.

A cewar Mataimakin shugaban NDDC Joi Nunieh ya ce shirin (LIFE-ND) shirin zai dauki tsawon shekaru 12 sannan hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC) da Asusun raya aiyukkan noma na kasa da kasa (IFAD) za su hada hannu domin samar da kudaden da za a kashe a wannan shirin.

Mataimakin shugaban NDDC Joi Nunieh ya ce shirin (LIFE-ND) a karshe yi kira ga mutanen yankin da su mara wa wannan shiri baya sannan kuma yayi alkawarin kirkiro irin haka a sauran yankunan Nijeriya.

A wani bangaren kuma, Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta samar da tsare-tsaren da za su inganta fitar da amfanin gona da aka noma a kasar nan zuwa kasuwannin duniya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, inda Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir ya sanar da hakan ne a hirar sa da manema labarai a Babban Birnin Tarayyar Abuja, inda Dakta Kabir yaci gaba da cewa, kalubalen da ke a cikin fannin aikin noma suna da yawan gaske, harda gazawar samarwa da manoman kasar nan samun damar fitar da amfanin su da suka noma zuwa kasuwannin kasashen ketare.

A cewar Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, har ila yau gazawar manoman kasar nan wajen cika sharuddan bukatun kasa da kasa na fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje da suka shafi lafiyar amfanin gonakan su, yana daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta wajen yin kasuwanci tsakanin Nijeriya fa da sauran kasashen ketare.

Manajan Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir yaci gaba da cewa, butar da ake da ita ga ko wannen dan Nijeriya ya rungumii fannin noma, ya kasance daya daga cikin, inda ya kara da cewa, tsarin Gwamnatin Tarayya na ERGP da akayi shi a bisa farfado da tattalin arzikin Nijeriya.

A cewar Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, Kamfanin na Wal-wanne ya kware wajen yin noma da kayan aiki na zamani, adana amfanin gona, da kuma yadda za a rabar da amfanin gona da aka noma a kasar nan kuma kamfanin yana yin kokari kan samar da ayyuakn yi ta hanyar noma ga alumomi da dama da ke Nijeriya.

Da ya ke yin tsokaci kan nasarorin Kamfanin Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir yace, Kamfanin na sarrafa Shinkafa Wal-wanne yana sarrafa Shinkafa tan-tan 120 a kulkum.

Ya ci gaba da cewa, Kamfanin ya samunasarar samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin mata da matasa, inda Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir ya sanar da cewa, Kamfanin ya tanadi tsare-tsare na bunkasa fannin noman Shinkfa ta hanyar yin amfani da kayan noma na zamani.

A cewar Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, ta hanya samar da wadannan dabarun yin noma da kayan aikin noma na zamani, mun samu sukunin kara bunkasa fannin noma a kasar nan, inda wasu amfanin gonar za’a iya fitar dasu zuwa kasuwannin kasashen waje don siyarwa idan akayi la’akari da dimbin bukatar da ake dasu a kasar waje.

A karshe, Manajin Darakata na rukunonin Kamfanin Wal-wanne Dakta Abiso Kabir, zamuci gaba da samar da ayyukan yi ta hanyar fannin noma, musamman a tsakanin matasan da ke kasar nan yadda suma za su zamo masu dogaro da kansu.

 

Exit mobile version