Daga Umar Faruk Birnin-kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ne ya bada umurnin a lokacin da ya kai wata ziyarar ba-zata a dakin ajiyar kayan kiwon lafiya na ma’aikatar lafiya ta jahir da ke a Birnin-Kebbi da kuma Bulasakazalika da Ni’ima Guest inn.
A nan take Gwamna Bagudu ya nada kwamitin bincike kan dukkan kwantenoni, Tireloli, da aka kawo a jihar ta Kebbi, wanda mai ba gwamna shawara kan aiwatar da ka’idojin aikin gwamnati, wato (Due Process) Alhaji Surajo Garba Bagudo a matsayin shugaban kwamitin., wakilai daga UNICEF, ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kebbi da kuma Hukumomin tsaro matsayin mambobi a cikin kwamitin, domin tabbatar da duk kayayyakin kiwon lafiya da aka kawo; an kawo su bisa ga ka’ida da kuma tabbatar da cewa akwai tsari a rubuce.
Sanata Bagudu ya bayyana cewa, ba ya tuhumar wani ko wata kan bincike, amma duba da la’akari da irin makudan kudin da Gwamnati ke sakawa wurin harkar kiwon lifaya, saboda haka Gwamnatin na bukatar sanin adadin kayayyakin da ake kawowa a jihar da kuma nawa ne kudaden kayan.
Harilayau Gwamna Bagudu ya nuna cewa, Gwamnatin ba ta da wani cikakken bayani kan yadda kayan ke shigowa jihar. Saboda haka rashin samun cikaken bayani kan yadda kayan ke shigowa da kuma yadda ake daukosu, wata matsalace babba kuma abin damuwa ne ga Gwamnati idan har ba ta samun cikakken bayanai tsakaninta da hukumomin da abin ya shafa.
Bugu da kari, gwamnan ya ce, bayar da bayanai na da matukar muhimmanci tsakanin Gwamnati da sauran hukumomin.Ya kara da cewa kudade ne da dukkan masu ruwa da tsaki ke bayarwa ga harakar kiwon lafiya ga cibiyar UNICEF.
Hakazalika ya umurci dukkan ma’aikatun gwamnati, hukumomin, da kuma kwamitocin a duka ƙungiyoyin da jama’ar Gwamnati da su rika rubuta duk wata ma’amala da suka yi da kyau domin ajiyewa a rijistocin Gwamnati da kuma ci gaba da rikodin don kaucewa abin da ke iya tasowa na yau da kullum.