Wasan E-classico shine babban wasan da babu kamarsa a kasar Spaniya, kuma zamu iya cewa yana daya daga cikin manyan wasannin da suke daukar hankalin mutane a duniya.
Kusan ya zamanto al’ada duk lokacin da za’a buga wasan hamayya na Elclassico baki daga kasashe daban daban na duniya suna zuwa kallon wasan, sannan kuma ko a gidajen da ake haska wasan kwallon kafa yana daya daga cikin wasan da yake tara masu kallo a wasu kasashen kuwa babu wasa kamarsa a shekara.
Wasan El-classico yana daya daga cikin wasan da yake karawa gasar laliga armashi domin yadda kafafen yada labarai suke zuzuta wasan sannan kuma wasan yana kara armashi ne sakamakon manyan yan wasan da suke kungiyoyin biyu, real Madrid da Barcelona.
A yan shekarun nan Cristiano Ronaldo da Leonel Messi sune suke haska gasar domin sune yawanci suke bajinta a wasan idan anzo bugawa.