Bello Hamza" />

Za A Fara Horas Da Karuwai A Abuja

Daga  Bello Hamza

Hukumar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta bayyana cewa, nan bada jima wa ba zata fara tsugunar da kuma horas da karuwan da aka kama suna gararanba a kan titunan Abuja a cikin wannan shekarar. Alhaji Ladi Hassan, Sakatare mai kula da jin dadin jama’a na babban birnin tarayya ya yi wannan tsokacin a tattaunawarsa da manema labarai a ofishinsa.

Hassan ya kara da cewa, bayan an kama karuwa bai kamata a barta ba tare da an tsugunar da ita ba tare da horas da ita sana’ar da zai taimaka mata dogaro da kanta, an shirya gudanar da horasawar ne a Sabon-Lugbe, ana fatan bayan samun horon zasu kyamaci harkar karuwancin.

“Aikinmu a wannan ma’aikatar shi ne tsugunar da horas da karuwai, da zaran an kamo su a kan tituna sai a turo manasu domin koyar dasu sana’o’in dogaro da kai domin su fuskanci rayuwa mai tsafta tare da barin sana’ar karuwanci”

A wannan shekarar 2018 mun shirya gagarumin aikin horas da karuwai, mun yi imanin cewa, idan aka kama karuwai to ya kamata a taimaka musu da sana’ar da zasu dogara da kan su ta yadda zasu nisanci sana’ar karuwanci” Ya kuma kara da cewa, bayan kammala horasawar da karuwan gwamnati za ta basu bashin kudaden fara sana’a, wanda hakan zai kara karfafa musu kauracewa wannan mummunan sana’ar na karuwanci.

Daga nan ya bayanna cewa, Hukumar ta shirya gyara matsugunin Kutare dake Yangoyi da na Makafi dake Karmajiji-Abuja, da kuma Sansanin Tsugunar da marasa galihu da ke Bwari da kuma wanda yake Nyanya.

 

Exit mobile version