DAGA HUSSAIN SULEIMAN, Kano
Gwamnatin jihar Kano ta kammala shirye-shiryen da suka kamata domin fara koyar da Cututtukan Mata zalla,GYNEACOLOGY inda an ware Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase, da aka fi sani da Asibitin Nasssara a zaman wurin da za a fara wannan koyarw da ake shirin yi nan da watanni Uku, inda kuma za a fara da dalibai kiminin 200.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban Asitin, Dakta Usman Aliyu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Dakta Usman ya ce, Domin ganin an samu nasarar shirin an gayyato manyan likitoci kwararru daga Kwalejin West African College of Surgeon dake kasar Laberiya, inda aka zagawa da su domi ganin shirin da aka yi na wannan koyarwar.
Dakta Usman Aliyu ya kara da cewa matukar aka fara wannan bada ilimi za a rika samun dalibai daga jihohin kasar nan suna zuwa karatun wannan fanni da ake karancin Likitoci akan shi.
Ya kara da bayyana cewa, Wannan shi ne karo na farko a cikin Asibitocin jihar da Gwamnati ta amince a fara, wanda zai dauki dalibai kimanin shekaru Biyar kafin su samu shaidar kammalawa.
Ya ce idan aka fara wannan shiri, Asibitin na Nassarawa zai iya gogayya da sauran Asibitocin Gwamnatin Tarayya da yardar Allah,
Ya kara da cewa abin farin ciki har an fara samun wasu Likitoci da dalibai da suka fara nuna sha’awarsu da zarar an fara karatun , an kuma tanadi kwararrun Malamai da suka yi fice akan wannan fanni.
Sai ya yi amfani da wannan dama da kira ga wadanda za su fara karatun da su mayar da hankali sosai akan abin da za koya masu ganin cewa Ilimi ne a ake bukatar shi a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara.
Matashin Likitan ya gode wa daukacin wadanda suka taimaka aka samu nasaran gudanar da shirin, musamman kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Kabir Ibrahim Getso, da shugaban hukumar kula da Asibitoci na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa,da kuma daukacin manya da kananan likitoci da ma’aikatan Asibitin .
Daga karshe ya gode wa Gwamnan jihar Kano game da gudunmawar da ya bayar wajen aiwatar da wannan shirin, tare da tallafa wa harkokin lafiya a daukacin Asibitocin jihar manya da kanana.