DAKTA ABDULLAHI IBRAHIM shi ne babban Daraktan gudanarwa na babban asibitin gwamnatin tarayya (Federal Medical Centre Azare) cikin tattaunawarsa da HAMZA ABUBAKAR kwanakin baya ya bayyana wasu daga cikin ci gaban da aka samu a asibitin tun da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta karɓi ragamar shugabancin ƙasar nan ga yadda tattaunawar ta kasan ce kamar haka.
Za mu so ka fara gabatar da sunanka?
Dukkan godiya ya tabbata ga Allah maɗaukacin sarki kamar yadda aka sani sunana Dakta Abdullahi Ibrahim shugaban asibitin gwamnatin tarayya dake garin Azare ‘Federal Medical Centre’ wannan asibiti yana daya daga cikin jerin asibitocin gwamnatin tarayya dake shiyyar arewa maso gabas kuma ba mutanen jihar Bauchi kaɗai ne suke amfana da asibitin ba.
Har da jihohin Jigawa,Yobe,Borno,Gombe dama jihar Bauchi kanta kuma tun lokacin da aka bashi ragamar shugabancin asibitin an samu gagarumin ci gaba da fannoni-daban-daban akwai ma’aikatanmu da dama da muka ɗauki nauyinsu domin karo ilimi a wasu sassan na daban.
Domin ba zamu iya gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata ba sai mun samu haɗin kai daga wajen al’umma baki ɗaya.
Aikin kiwon lafiya aiki ne dake buƙatar haƙuri da juriya kuma tsakani da Allah babu abinda zamu faɗawa ɗaukacin mutanen garin Azare sai Allah ya saka musu da alheri domin suna bada dukkan goyon bayan da ya kamata ga wannan asibiti na gwamnatin tarayya.
Waɗanne matsaloli kuke fuskanta a Asibitin a halin yanzu?
Tsakani da Allah babu wata matsala da muke fuskanta a wannan asibiti a halin yanzu domin gwamnatin jihar Bauchi a ƙarƙashin gwamna Mohammed Abubakar da ma’aikatar lafiya ta jihar Bauchi suna bamu dukkan goyon bayan da ya kamata.
Kwanakin baya hukumar gudanarwa na wannan asibiti mun kai ziyara ga gwamna Mohammed Abubakar a gidan gwamnatin jihar Bauchi inda muka tattauna abubuwa masu ɗimbin yawa.
Amma mun koka masa game da batun injin jannareto da muke nema kuma ya mana alkawari zai bamu amma har yanzu saƙon bai shiga hannunmu ba amma muna da tabbaci zai cika wannan aikawari da ya ɗauka.
Akwai ɗan majalisa daga wannan yanki na Azare Honarabul Ibrahim Baba inda kwanakin baya ya bamu ƙyautar sabuwar motar ɗaukar marasa lafiya tare da magani da gadaje da sauran kayayyakin amfanin asibiti muna masa godiya da sauran waɗanda suke bada gudunmawa ga wannan asibiti.
Ita kanta ma’aikatar lafiya ta ƙasa a ƙarƙashin babban ministan lafiya Farfesa Adewale tana bamu dukkan goyon bayan da ya kamata kuma muna da sabbin injina na zamani nan da watanni kaɗan masu zuwa zamu buɗe manyan gine-ginenmu dake cikin wannan asibiti ta FMC Azare.
Kuma nine shugaban shugabannin asibitocin gwamnatin tarayya duk lokacin da za a zauna da ministan lafiya ƙarami ko babba nine nake jagorantar zaman kuma kwalliya tana biyan kuɗin sabulu daidai bakin gwargwado.
Gwamnatin tarayya tana bada dukkan kayayyakin da ya kamata ga asibitocinta dake sassa daban-daban na ƙasar nan domin ni ne shugaban shugabannin asibitocin gwamnatin tarayya.
Babban abinda muke nema a wajen al’umma shi ne su taimaka mana da addu’oi domin shugabanci yana da matuƙar wahala.
Tun lokacin da Allah ya yi rasuwa Dakta Musa Muhammed Damban na karɓi ragamar shugabancin wannan asibiti kuma mun ci gaba da ɗora ayyukan alheri na Dakta Musa Damban daidai bakin gwargwado.
Muna da kayyakin aiki na zamani wanda ko a ƙasar turai iya kayayyakin da za su yi amfani da shi ke nan an samu sabbin gine-gine da sauran kayayyakin aiki na zamani har da sabon injin dake gwada kwakwakwa a cikin asibitin.
Wanne saƙo ka ke da shi ga ma’aikatan asibitin nan?
Babban saƙona ga ɗaukacin ma’aikatan wannan asibiti shi ne kowa ya ci gaba da kula da aikinsa sannan kuma a ci gaba da haƙuri da jama’a domin haka aikinmu ya gada dole sai mutum ya kai zuciya ne sa kafin a samu ci gaba.
Wannan gwamnati ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tana da manufofi masu ƙyau a fannin kiwon lafiya amma ba kowa zai fahimci haka sai wanda yake sashin kiwon lafiya na asibitocin gwamnatin tarayya.
Sarkin-Ban katagum Alhaji Adamu Bulkaciwa yana ɗaya daga waɗanda suke kawo gudunmawar magunguna ga wannan asibiti daga lokaci zuwa lokaci kuma babu abinda zamu faɗa masa da sauran mutanen garin Azare sai Allah ya sakawa kowa da alheri.
Har yanzu muna neman gudunmawar motoci da sauran kayayyakin aiki a wannan asibiti na FMC Azare kuma kafin ƙarshen wannan shekara ta 2017 zamu kaddamar da sabbin gine-ginenmu dake cikin wannan asibiti na gwamnatin tarayya.