Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi, reshen Babban Birnin Tarayya Abuja (ALGON), Hon. Joseph Shazin Kwau ya bayyana aniyasu ta ba da goyon baya ga ƙungiyoyin da ke tallafa wa cigaban matasa ta kowace fuska.
Shugaban ƙungiyar wanda har ila yau shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwali, ya bayyana haka a sa’ilin da ake bikin ƙaddamar da Ƙungiyar Matasa Masu Shan Shayi (Shayi Youth Association) a Gwagwalada.
Wanda mai taimaka masa na musamman a kan yaɗa labarai, Alhaji Iya Pai ya wakilta, shugaban na ALGON ya bayyana cewa kasancewar matasa ƙashin bayan cigaban al’umma suna buƙatar a ƙarfafa musu gwiwa kan aikace-aikacensu da za su kawo haɓakar tattalin arziƙi da kwanciyar hankali a tsakanin jama’a.
“Kamar yadda kuka sani, shi Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwali tsohon malamin makaranta ne, ya yi ciyaman a baya, a yanzu kuma aka sake dawo da shi saboda ƙwazonsa. Shi mutum ne mai ba da goyon baya ga ƙungiyoyi domin su iya dogaro da kansu. Kamar yanzu a Kwali akwai ƙungiyoyi da yawa da yake taimaka masu da wasu abubuwa da za su ƙarfafa su”.
“Idan matasa suna da abin yi ba za a samu aikata munanan laifuka ba, za ka ga sun mayar da hankali kan abin da zai amfane su. Rashin sana’a yake kawo duk abubuwan da ba su dace ba a wurin matasanmu. Shi ya sa saboda muhimmancin wannan taron ya shirya da kansa zai zo sai kuma wani uzuri ya faɗo. Amma ya umurce ni in koma in shaida masa duk abin da ya gudana a wannan taron kuma zan isar masa da yardar Allah”. In ji shi.