Khalid Idris Doya" />

Za Mu Ba Da Gudunmawa Don Daukaka Kimar Masarautar Bauchi, Inji Sabon Hakimin Miri

HUSSAINI ABUBAKAR OTHMAN Shi ne Sabon Hakimin Kasar Miri da ke jihar Bauchi wanda aka masa wankan nadin Sarauta a ranar 27 ga watan Maris, 2020; A bisa haka ne manema labaru ciki har da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, KHALID IDRIS DOYA suka nemi ji ta bakinsa bayan nadin da aka masa inda ya sha alwashin hada karfi da karfe wajen kiyaye daraja da mutuncin Masarautar Bauchi. Ga hirar daki-daki:

Ga shi Allah ya baka sarautar Hakimin Miri ya ka ji, sannan wasu matakai ka taka wajen kai wa ga gaci?

Na farko ina godiya wa Allah saboda abu ne da na dade ina fafutukar neman, Hakimta wancan karon da aka bani Dagaci, Hakimi na nema amma ban yi nasara ba aka maida Hakimtan ta koma Dagaci, aka zo aka samu wata gwamnati ta ce ba za ta yi tafiya da mu ba, ta ciremu. An yi gwagwarmaya sosai gwagwarmayar neman Sarauta ba wani abu ba ne da ake yadawa, abu ne da addu’a kawai zaka yi ta yi kuma ksamu wanda zaka yi kamun kafa da su don su tuntudi masu ruwa da tsaki akan harkan Sarautan. Abu mafi muhimmanci duk wadanda muka yi takaran nan da su ina basu hakuri da su san cewa haka al’amarin Allah yake, duk abu na takara mutum daya ne ya ke ci, sauran ba za su ci ba, bawai ba su kai aba su ba ne, a’a rabo na wannan wani lokaci wani ne da rabo, ni kenan. saboda haka ina kira garesu mu hada kai mu hada hannu mu ci yar da Masarautan Bauchi gaba.

Tarihi ya nuna ka nace kana neman Hakimanci wai meye daliln hakan?

Saboda na samu daman da zan iya aiki da tunani na domin idan baka da mulki tunanin ka da kake yi ba zai yi aiki ba, sai dai a gidanka. Ni ina ganin cewa tsarin sarauta ya kamata a ce ita ce zata gamsar da mutane a wajen jagoranci fiye da kowani irin yanayi. saboda kun ga maigida shine shugaban gidansa idan Gidan sukayi yawa sai a samu mai unguwa idan masu unguwan suka yi yawa sai mai littafi wanda shine mai kula da masu unguwanni, daga nan sai a sake haurawa sama a samu mai gunduma ko kuma Dagaci daga nan sai a sake haurawa a samo Hakimi daga nan kuma sai Sarki; kun ga wannan tsarin yana da kyau ya zamto cewa an rayashi. Abin da ya sa nake neman sarauta shine wannan tsarin ‘yan zamani basu fahimceshi ba, amma shi ne tsarin da ya dace da al’adun mu ya kuma dace da tsarin rayuwar mu, shine za a iya sanin abunda kowani gida take ciki a kowani rana. Yanzu abun da na ke kokarin yi har na fara sayan kayan aiki, zan samar da na’ura mai kwakwalwa (kwamfuta) ma kowani Dagaci guda daya kuma zan dauki sunayen duk ‘yan wannan Guduma din, zan bada abunda za ana kawo korafi domin a san damuwowin mutane, kamar yanda tsarin yake haka umarnin zai gangara har kasa.

Za mu bunkasa karatu da neman ilimi domin  mu na so mu rika sanin yara sun tafi makaranta? ya yanayin karatunsu? tun daga ajin reno na Nursery har zuwa sama, saboda duk wanda ya haifi ‘ya’ya baya kula da su bai sa su a makaranta ba, bai koya musu sana’a ba, kawai ya haifi dan sara-suka ne,  ba zamu yarda da wannan ba dole a dauki mataki, akwai tsare-tsare masu tarin yawa da nake da su, lokaci ne zai nuna yanda za mu aiwatar.

Ta wasu hanyoyi za ka iya bunkasa yankin da kake mulka?

Ita sarauta gaba dayan ta harka ce ta sadaukar da kai. Zan samu kudin wadannan ayyuka ne da kudin da tunda nake rayuwa da su,  sannan kuma idan na samu mutanen da suka aminta da abin da nake so sai su taimaka a ciki, ba zan tunkari gwamnati na ce ina neman wani abu, idan na rubuta wannan ya zama kamar ban shirya ba kenan tunda yanzu gwamnati tana da matsala wajen kudi, wasu ta yiwu suna ganin kamar mafarki ne wanda ba zan iya cimmawa ba amma lokacin dana aiwatar aka ganshi zahiran mai yiwuwa mu zama wadanda za a yi koyi da mu har gwamnati ta iya shigowa ciki ta taimaka amma Insha Allah na himmatu zan yi wannan  aikin.

A wannan karnin Sarauta tana samun koma baya musamman ganin cewa masu mulki na gwamnati su ne suka fi masu sarauta iko ya kake ganin za a dawo da martabar masarauta?

Yadda za a dawo da martabar Masarauta shine na farko kar Basarake ya je ya shiga hidiman gwamnati inda zai kawo rigima tsakanin Basaraken da gwamnati, kullum Basarake yana goyon bayan gwamnati, ina ganin kamar abinda yake kawo rigima tsakanin gwamnati da Masarauta shine Sarakan ne suke kokarin nuna karfinsu har ya wuce na iyayen gidan su, idan aka yi wannan kuwa za a samu rigima.

An ce kowani abu na da hurumi a dokokin tsarin mulkin kasa Masarautun Gargajiya kuma ba su da hurumi ba ka ganin wannan shi yake kawo rigima?

Idan kana son jin ra’ayina wannan kira da ake yi na cewa a sa Sarakai a cikin tsarin mulki ni bana goyon bayansa, saboda idan aka sanya Sarakai a cikin gwamnati dole su zama karkashin wata ma’aikata wani lokaci shugaban wajen yana girmama Sarauta wani lokaci kuma za a samu wanda baya girmama Sarauta, kuma duk lokacin da aka ce an sanya Sarki a wani tsari ana turo masa kudi, bincike zai taso, cin mutunci zai taso, shi ya sa bana goyon bayan wannan. Amma yanzu da aka yi wa Sarakuna haka sai na ga aikin su ya fi yawa domin yanzu gyaran zumunta aikin Sarki ne, aikin addini aikin Sarki ne, bada shawara wa gwamnati aikin Sarki ne, a yi addu’a gari ya samu zaman lafiya aikin Sarki ne, akwai abubuwa da yawa wadanda duk aiki ne na Sarki, amma yanzu da zarar an shata wani abu sai a ce nanne kawai huruminsa ka ga an iyakance shi kenan, amma yanzu duk abinda ake bawa Sarki ana ba shi ne maimakon Masarauta. Kuma Sarki shine mutumin da yake da karbuwa a wajen kowa da kowa duk abin da yanzu ya kira na wadatan kasarsa ya ce su taimaka a yi abu kaza indai an saka amintattu wanda mutane suka yi na’am da su wallahi za ka ga aiki na tafiya.

Ya lamarin tsaro take a Masarautarka?

Alhamdulillahi akwai tsaro, yanzu ma haka ana jirana zan je wani taro na tsaro, shi aikin tsaro shine babba kuma Alhamdulillahi ana yi, yanzu ka ga ta wajen Yelwa wasu yara sun tashi za su kawo wa mutane irin tsageranci na Sara-Suka amma Allah ya bamu dama an cafkesu suna hannun ‘yan sanda, za a kai su kotu, ba mu sake da kowani labari komai kashinsa. Domin abinda ya kama daga kan masu littafi masu unguwanni sun fi mutane ne sama da dari biyu a masarautar nan banda sauran nade-naden fadodi idan ka kara sun kai dari biyar wanda kowannen su ma’aikaci ne na masarautar ana fada mana sakonni cikin dare koda rana, mu kuma muna daukan mataki, kuma muna addu’a sosai muna neman taimakon al’ummarmu da suke taimakawa mana da bayanai masu amfani kuma da addu’a.

Yanzu idan masu karatu suna son sanin cikakken tarihinka me zaka ce da su?

Sunana Hussaini mu tagwayene ina da Hassan dina sunan mahaifinmu Abubakar shi kuma sunan mahaifinshi Usman, Usmanu shi ya fara sarautan Wali a Masarautar Bauchi. An nadashi a zamanin Sarkin Bauchi Maigari, a lokacin Babansa shine Yakubu Maigari, shi mahaifin Kakan nawa yayi takaran sarautar tare da Yakubun Bauchi, Allah ya bada nasara wa Yakubu Maigari dan Usmanu. bayan Yakubu Maigari yayi nasara sai ya dauko babban dan abokin takaransa na sarauta dan Mallam Ghani, domin idan ka ji an ce mutum Maigari a Bauchi to sunan Yakubu ne, shine ya dauko babban dan abokin takaransa ya bashi Sarautar Wali. Shi aikin Wali mutum ne mai tsage gaskiya a Fada kuma ba za a bada Wali wa mutum ba sai masanin addini, Masanin Shari’a, sannan kuma aikin da aka kara masa da shine ke lura da ayyuka da Turawa suke yi na raya yankuna da birane a lokacin, shi ya lura da aikin tsohon gadar Kari wanda ta hadu da Misau duk Kakana Walin ne ya lura da aiyukan.

Sannan wanda ya haifeshi shine Maigari dan Malam Ghani wanda ya haifi Maigari dan Malam Ghani shine Mallam Muhammadu Ghani, shi kuwa Mallam Muhammadu Ghani dan Malam Yakubu ne saboda haka ka ga a gidanmu Muhammadu Ghani shine tushen gidan domin shine dan aika na Malam Yakubu mu ne gidan Muhammadu Ghani kuma Muhammadu Ghani dan Malam Yakubu Ghani ne, asalinmu dai zuriyar Malam Yakubu ne wanda ya kafa Bauchi.

Ta bangaren karatunka fa?

Karatu mun taba kadan. Na farko na fara karatun Alkur’ani a wajen Malam Sani na Tura shi Malam Sani na Turan nan shine mahaifin Lawan Tura mai Fartanya shine mahaifinsu babban Malami ne a wajensa, muka fara karatu bayan rasuwansa sai muka koma wajen kakanmu sunansa Malam Umaru daga nan sai mahaifinmu ya bude makarantan dare, wanda ya sa mata suna Madarasatul Arkanul Islami, yana karantar damu Tauhidi da Fikihu da karatun Alkur’ani, lokacin makarantun Islamiyya a Bauchi ba su da yawa. daga nan sai kuma muka je makarantar Malam Ahmadu sabon gida Baban su Malam Abdulmajidu a bayan Fada muka yi karatu, daga nan muka je wajen Malam Hamidu Sarkin Zungur lokacin Malam Adamu Jumba ya bude aji na karatu, a tsohon masallaci mu ne dalibai na farko, daga nan kuma na shiga makarantan Mallam Baba Karami a lolloki Mahaifin Marigayi Malam Bala Baba Karami da su Malam Tanko Baba Karami shi yana da rai na yi karatun addini a wajensu.

Sai bangaren boko na shiga makarantan boko a 1968 a Shekal Primary School a 1970 aka fito da wani abu wai shi daukan darussa da yamma da ake kira ‘ebening classes’ a turance, saboda cinkoson yara kuma gwamnati ba za ta iya kara yawan ajujuwa ba, a lokacin, sai aka raba makarantan gida biyu aka debe rabi aka maida su makarantar Firamare na Kobi, ni ina cikin wadanda aka maidasu Kobi muka yi muka gama a 1975. A wancan lokacin samun daman shiga sakandare indai baka ci jarabawa yana da wahala sai na dawo zan sake maimaita makarantan na fara a makarantar firamare dake kofar Fada wato ‘Fada Primary School’ daga nan na bari na samu shiga wajen koyar da sana’o’i na karanta ‘Electrical Installation’ daga nan aka dauke ni aiki a ma’aikatar aiyuka da fusuri a fannin wuta, amma da na dan taba aikin kadan har na samu Grade 1 sai na yi sha’awan na je na yi zaman kaina, saboda a lokacin matsalar dana lura da ita cikin aiki  wanda  bana so shi ne ku zauna ba aiki, sai ku yi sati baku fita aiki ko’ina ba, na ce ni bana sha’awan wannan.

Na rubuta takarda na ce na ajiye aiki a 1985, na fita har zuwa yau da aka bani sarauta amma na yi karatu a wata makarantan kwaleji mai suna Jama’atu College a Zariya wanda suna da hadin gwiwa da Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya (ABU), saboda Jami’ar ne suke bada takardar shaidar kammala makarantar, ni abinda na karanta a wajen ba Diploma ba ne, amma satifiket ne mai kwari domin karatun da ake yi a wancan lokacin koyan diploma ba a musu ina da wannan. Baya ga hakan kuma saura neman ilimi nan da can shine abin da nasa a gaba da kuma aikin wa’azi. Bayan haka sai na tsunduma aikin jarida.

Mune muka kafa wata jarida mai suna Almizan bayan da muka samu matsala da Jagoran muka dare gida biyu, muka kafa wata Jaridar ana ce mata Attajdid, ba karanta aikin jaridar na yi ba amma koya na yi a zahirance a wajen wanda suka karanta wannan ya bani dama lokacin da aka zo siyasar Malam Isa Yuguda na fitar da wata jarida mai suna ‘Bauchi Lokaci Ya Yi’ nine Edita din jaridar, ni nake komai wannan ya sa na kara gogewa a fagen aikin jarida dama can akwai wanda muka zauna da su kuma mun kira kwararru a aikin sun mana darasi a wancan lokacin da muke da Attajdid din wannan ya sa muka fahimci sirrin yanda aikin ke gudana.

Lokacin da kake da’awa wasu irin ayyuka kuke yi a cikin da’awar?

Masu Da’awan iri biyu ne domin akwai masu shigo da sababbi cikin musulunci  da masu gyara tsofaffi, ni ina bangaren masu gyara tsofaffi ne, wato su musulmi kamar yanda Allah ya ce; “Ya ayyuhal lazina amanu aminu billahi wara sulihi” ka ga masu imanin ma ana so su kara musu imani, wannan shine abinda na dinga yi nasa mu mutane da suka musulunta ta hannu na ban san iyaka adadin su ba, amma karantarwa a karantar da mutum da addini  ko a koya masa baki ko a koya wa mutum karatun Alkur’ani wannan ban san adadinsu ba.

Kawo yanzu iyalanka nawa?

Ina da mata hudu ‘ya’ya kuma ashirin da biyar, da su ashirin da shida ne kwanan nan daya ya rasu Allah ya gafarta masa maza goma sha biyu mata goma sha uku, ka ji iyalai na.

Wani fata kake da shi ganin cewa an samu na ci gaba a wannan masaurata taka kuma wani kira zaka yi wa al’ummar masarautar?

Fatan da nake yi shine a samu ladabi da biyayya a wannan masarauta kuma ‘ya’yan masarauta su rungumi abin yi komai kashinsa, a ce mutum yana da abin yi shi ma akwai ababen da muka shirya wanda zamu wayar da kan mutane su tashi su nemi abin yi, zai yi kyau bayan shekara biyu ko uku idan muna da rai ku ga cewa abin da na ke so na yi daga yanzu zuwa wannan lokacin shine abinda shi na ke so na cimma yayi daidai da abinda na cimma ko bai yi ba. shawaran da zan baiwa al’umma shine mu zamo masu ladabi da biyayya masu abun yi a rayuwa kuma mu zamo masu kokarin kawo ci-gaba mutum yayi fafutikan wani abu da tarihi ba zai manta da shi ba .

Gwamnati fa?

Ita gwamnati ina ba ta shawara ta saurari kiraye-kirayen da talakawanta suke mata domin ta biya musu bukatunsu kuma za mu ci gaba da sanar da mutane da wayar musu da kai su zamo masu ladabi da biyayya da bin gwamnati, idan mutum yana da koke ya bi hanya mai tsafta wanda ya bi aka gudanar da koken kuma muna kira ga jama’a su yi ta addu’a wa mai girma gwamna Allah ya shi lafiya ita ma jihar mu na Bauchi da kasanmu Nijeriya Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya sannan mai martaba A Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, Allah Ubangiji ya kara masa lafiya da kuma himma akan wannan aiki na shugabancin al’umma.

Exit mobile version