Daga Zubairu M Lawal,
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da wadatattun kudade, a matsayin taimakawa na bayar da tallafi ga Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta (UBEC), don magance karancin kayayyakin makarantar, kayan aikin koyarwa da kuma gyara wasu makarantun Gwamnati da suka lalace.
Gwamna Abdullah Sule ya bayyana hakan ne a yayin bikin rantsar da sabon shugaban da aka sake nadawa Alhaji Muhammad Dan Azumi da sabbin mambobi uku na Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Jihar Nasarawa (NSUBEB).
Yayin da yake sake nanata kudirin Gwamnatin sa na samar da ingantaccen ilimi ga yara a jihar, musamman a matakin firamare, Gwamnan ya ce ya bayyana dalilin da ya sa Gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da wadatattun kayan aiki wajen biyan takwarorin na su.
Wannan zai taimaka wajen samar da karin kayayyakin aiki a makarantu, kayan aikin koyarwa na Ilumi mai inganci wadanda ake bukata don samar da kyakkyawar yanayi mai kyau don koyarwa da koyo mai inganci a makarantun jihar.
Gwamnan ya ce ta irin wannan gagarumar saka jari a bangaren ilimi, jihar za ta samu karfi da kwarewar da ake bukata don ci gaban ilimin dalibain makarantun Gwamnati da na masu zaman kansu.
Gwamna Sule ya ce kaddamar da mambobin kungiyar ta NSUBEB, zai kara karfafa bangaren ilimi a gaba cikin jihar, da kuma samun cigaba da kokarin da Gwamnatin ke yi na sake sanya makarantun firamare da kananan makarantun sakandare a matakin farko na Ilumi.
“Tsarin Gwamnatin mu za ta cigaba da dagewa wajen samar da ingantaccen ilimi ga yaranmu, musamman a matakin firamare, domin samar da ginshiki mai karfi na kula da su har su zama shugabannin gobe na gaba,”
Gwamnan ya kara da cewa biyan takwaransa kudade, ya baiwa NSUBEB damar samun kudaden da suka dace daga UBEC, wanda hakan ya haifar da gagarumin gini da gyara makarantun firamare da sakandare a fadin jihar Nasarawa.
“Wannan kokarin guda daya, na yi imanin, zai magance wasu matsaloli da dama da suka hada da karancin kayayyakin aikin koyarwa da lalacewar wasu makarantunmu.”
Gwamnan ya kaddamar da Muhammad Musa Da’azumi a matsayin Shugaban NSUBEB a karo na biyu.
Kaddamar da Kanar Jibrin Bala Yakubu (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Nasarawa, Gwamnan ya ce, wannan zai karfafa hukumar don gudanar da aiki yadda ya kamata.
Gwamna Abdullah Sule ya ce wadanda aka nada din an zabo su ne bisa la’akari da kwarewarsu, da aiki tukuru, sadaukarwa, kishin kasa da kuma asalinsu, yana mai umurtar su da su yi aiki domin cigaban wannan jihar.
Ya dora musu nauyin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, ba tare da wani tunani ko son kai ba.
Gwamnan ya yi amfani da damar taron wajen jinjina wa kakakin majalisar da kuma mambobin majalisar dokokin jihar saboda saurin lura da wadanda aka zaba da kuma nuna kyakkyawan jagoranci da kuma hada kai don cigaba da aiki tare cikin jituwa don isar da alheri ga mutanen jihar.
Gwamnan ya kuma yaba wa wasu gungun da suka tallafawa Gwamnatin sa, musamman Bankin Keystone, Bankin Guarantee Trust (GTB) da Babban Bankin Najeriya (CBN).
Bankin Keystone ya inganta makarantun kimiyya a fadin shiyyoyin majalisar Dattijai guda uku a jihar, GTB ya fara inganta yawancin makarantu a shiyyar sanatocin Kudancin, yayin da Gwamnan babban bankin na CBN da sauran jami’an bankin koli, suka yanke shawarar karbar mafi yawan makarantu. harda Kwalejin Gwamnati ta Keffi.