Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Soceidad, David Silva, ya bayyana cewa kungiyar zata ba wa duniya mamaki a kakar wasan bana sakamakon irin kokarin da kungiyar ta ke yi na ganin ta lashe gasar La liga ta bana.
Sai dai Real Sociedad sun kasa ci gaba da zama a saman teburin La Ligar a daren Lahadin data gabata bayan da abokan hamayyarsu Alabes suka rike su canjaras sai dai Sociedad tayi wasan ba tare da kyaftin dinta ba, Mikel Oyarzabal, wanda yake jinyar raunin da ya ji, sun kasa ratsa bayan Alabes.
Tashi wannan wasa ba ‘kare bin damo’ da suka yi ya kawo musu koma baya da maki daya, a bayan Atletico Madrid, wadanda suka lallasa Real Billadolid da ci 2-0 a nasara ta 7 a jere a gasar La Liga.
“Wannan shekarar shekararmu ce domin za muyi kokarin ganin mun bawa marada kunya kuma za muyi iya kokarin mu na ganin mun lashe gasar La liga saboda ina ganin a wannan kakar komai zai iya faruwa” in ji Silba, tsohon dan wasan Manchester City.
Real Sociedad da Billarreal sun fi Atletico da yawan wasanni 2, sun kuma fi Real Madrid da ke matsayi na 4 da yawan wasa guda sai dai suma Real Madrid sun kyauta wa kansu da nasara daya da nema a kan Sebilla ranar Asabar.
Publicit
Cadiz wadanda a wannan kaka suka samu ci gaba na zuwa gasar La Liga su na matsayi na 5 a teburin gasar, bayan doke Barcelona 2-1 a Asabar, abin da ya kai Barcelonan, da matsaloli suka yi musu katutu matsayi na 9 a gasar kasar Spain din, kuma rashin nasararsu ta hudu kenan a wannan kaka.