Za Mu Ci Gaba Da Amfani Da BVN Wajen Bai Wa Talakawa Tallafi- Minista

Gwamnatin tarayya ta ce za ta fadada tallafin da take bayarwa ga Talakawa ta hanyar amfani da fasahar zamani wacce ta hada lambar sirri ta asusun banki na BVN domin bankado Talakawa domin tura musu na su tallafin.

Ministar Tallafi da jinkai, Sadiya Farouq ce ta bayyana hakan a Abuja a ranar Talata a yayin da take amsa tambayoyi ga kwamitin da shugaban kasa ya kawwana kan lura da dakile yaduwar cutar  Koronabairos a Nijeriya.

CHANNELSTV ta labarto Ministar na tabbatar da cewa za su yi amfani da fasahar zamani wajen bada wannan tallafi, inda ta ce hakan ma zai fi saukin isa ga Talakawan ba tare da wani targarda ba.

Ta ce; “Muna amfani da BVN da kuma lambar wayoyi domin bankado marasa galihu a cikin al’umma ganin sun amafana da wannan tallafin.”  Inji ta.

Ministar ta ce; wannan tsarin na su ya fi sauri, da kuma kasancewa cikin gaskiya, kuma zai fi saukin a yi bincike a kai domin gano yadda aka yi rabon.

Sai dai ta tabbatar da cewa shirinsu na bi gida-gida suna rabawa Talakawa kudi a wadansu sassan kasarnan shi kansa ana bin ka’ida ne yadda ya kamata, kuma ta ce yana tafiya cikin gaskiya da tsari. Sannan ta ce gwamnatin tarayya ta bi dukkannin matakan da suka dace wajen ganin ba a maimaita tallafin ga gida daya ba.

Sannan ta tabbatar da cewa; suna amfani da Sarakuna da sauran kungiyoyin al’umma wajen bankado Talakawan domin ba su tallafin gwamnati.

 

Exit mobile version