Za Mu Ci Gaba Da Samun Nasara Duk Da Babu Messi -Buskuet

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Sergio Baskuet ya bayyana cewa kungiyar zata ci gaba da samun nasara a wasanninta duk da cewa dan wasa Leonel Messi yaji ciwo

Lionel Messi ba zai samu damar buga wasan hammaya na El Clasico da kungiyarsa Barcelona za ta fafata da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid ba a ranar Lahadi mai zuwa a filin wasa na Nou Camp.

Messi ba zai samu buga wasan na El Clasico bane a dalilin raunin da ya samu a wasan gasar La Liga da Barcelona ta lallasa Sebilla da kwallaye 4-2 wasan daua zura kwallo a raga kuma ya taimaka akaci kafin yaji ciwon.

“Za mu iya ci gaba da samun nasara duk da cewa babu Messi amma baza mu taba buga wasa kamar ace yana cikin fili ba saboda babban dan wasane kuma yanada tasiri a wasa amma kuma dan wasa baifi kungiya ba” in ji Baskuet

Dan wasan na Barcelona ya samu raunin ne, bayan faduwa kan hannunsa na dama da yayi, a lokacin da suke kokarin daukar kwallon tsakaninsa da dan wasan Sebilla Franco Bazkuez, hakan ya tilastawa Messi ficewa daga wasan na ranar Asabar ba tare da an kammala ba.

Bayan kammala wasan ne, Barcelona ta bada tabbacin cewa dan wasan nata mai shekaru 31, ya samu dan tsagewar kashi a hannu, dan haka ba zai samu buga wasan El Clasico da Real Madrid ba, zalika ba zai samu buga wasan gasar zakarun turai da Barcelona za ta fafata

Exit mobile version