Ibrahim Muhammad">

Za Mu Cigaba Da Ayyukan Bunkasa Rayuwar Al’ummar Bagwai – Inuwa Zangina Dangada

Shugaban Karamar Hukumar Bagwai, Alhaji Inuwa Zangina Dangada ya yi alkawarin cigaba da gudanar da ayyukan raya kasa domin cigaba da bunkasa rayuwar al’ummar yankin.

Ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya maye gurbin tsohon shugaban karamar hukumar Hon. Yusuf Badau wanda ya zama zababben dan majalisar tarayya. Cikin dan kankanin lokaci ya sami nasarar gudanar da ayyuka da dama dan tallafa wa rayuwar al’ummar karamar hukumar ta Bagwai.

Hon. Inuwa Zangina Dangada ya ce, cikin muhimman ayyuka da ya gudanar sun hada da gina gadar Yalawai da ta hade karamar hukumar Bagwai da ta Bichi.

Dangada ya kara da cewa yasa an samar da wutar lantarki a wasu  mazabun yankin da suka hada da Wurabaggo,Gogo ,Sari-sari da Gadanya da sauran wurare da a baya tun sama da shekaru 9 ba su da wutar lantarku sai a zuwansa yanzu.

Ya ce, akwai gyaran wutar lantarki da aka yi a mazabar Rimin-Dako. Sannan akwai aikin samar da ruwansha da Gwamnatin jihar Kano a Bagwai a lokacinsa na gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da aka samar a Dangada da Wurabagga, Gadanya, Kwajale, Bagwai da Kiyawa.

Alhaji Inuwa Zangina Dangada ya gode wa Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Kano. Hon. Murtala Sule Garo wanda da sahalewarsu da irin goyon baya da suke bashi ne ake samun cigaban karamar hukumar Bagwai.

Hon. Dangada ya kuma godewa ma’aikata da zababbu a kowane mataki da sauran masu ruwa da tsaki da al’ummar karamar hukumar bisa hadin-kai da goyon bayansu a gareshi wajen cimma nasarar gudanar da ayyukan raya cigaban karamar hukumar.

Exit mobile version