Daga Sulaiman Ibrahim
Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi ya bayyana cewa an kashe wasu sarakunan da masu unguwanni a yankinsa saboda jajircewa wajen tona asirin ‘yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.
Ya ce duk da kashe-kashen, baza su yi rauni ba, za su ci gaba da hada kai da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kuma jami’an tsaro don magance ‘yan ta’addan da basu son zaman lafiya ya dawo jihar da kuma yankin arewa maso gabas baki daya.
Ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawar sa da jaridar LEADERSHIP FRIDAY a fadar sa dake Maiduguri.