Connect with us

RIGAR 'YANCI

Za Mu dinke barakar Cikin Gida Kafin Zaben Shugabanninmu A Neja – PDP

Published

on

Shugaban jam’iyyar PDP na riko a Neja, Alhaji Garba Umar Chiza ya sha alwashin samar da shugabancin na gari a jam’iyyar dan sake samun damar karbe ragamar siyasar jihar. Shugaban ya bayyana haka ne a taruka mabanbanta da ya gudanar tare da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka kunshi iyayen jam’iyya da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi ashirin da biyar da shugabannin mata a sakatariyar jam’iyyar da ke minna.

Chiza ya cigaba da cewar mu a PDP kan mu daya ne, dan haka duk abinda ke faruwa a yanzu sabon salo ne na kafa shugabancin jam’iyya ta hanyar dimukuradiyya, mun yarda da dukkanin bangarori masu takarar shugabancin jam’iyya wannan ke nuna ma PDP ta kama tafarkin dimukuradiyyar a cikin gida wanda da irin wannan salon ne dimukuradiyya ke samun gindin zama yadda ya dace domin karfin kuri’a ne kadai ko amincewar ‘yan takara ne zai iya ba ka damar samun matsayi a jam’iyya.

Dukkanin bangarorin da muka zauna da su da suka shafi masu ruwa da tsaki na jam’iyya da shugabannin kananan hukumomi, matasa da mata kowa na da rawar takawa wajen hadin kai da tafiya tare da juna dan samun tsari mai inganci a tafiyar siyasa ba tare da nuna bambamcin yare, jinsi ko asali ba, a PDP duk daya muke.

Da ya ke karin haske ga manema labarai, tsohon karamin ministan cikin gida, Hon. Abubakar Tanko ( Acituwo) yace hanyar da aka dauko yanzu hanya ce mai inganci a siyasa domin wannan ne zai baiwa duk wani mai sha’awar shugabancin jam’iyya damar sanin irin rawar da ya kamata ya taka idan ya kai ga nasara.

Mu a PDP ba mu da bambamci kuma hanyar da aka tako tafiyar bai sabawa dokokin jam’iyya ba, sannan akwai damar zama tsakanin ‘yan takara dan yin yarjejeniya ba sai an kai ga jefa kuri’a ba, wanda wani na iya janyewa dan uwansa in kuma ma ba a samu wannan damar ba sai a tafi zabe wanda hakan zai iya baiwa duk wanda Allah ya baiwa nasarar da ya ke nema.

Hon. Tanko yace shugaban jam’iyyar mu na riko dattijo ne mai amana kuma muna da tabbacin cewar matsayin shi na almajiri zai jagoranci wannan amanar da aka ba shi da gaskiya domin ya rike matsayi na a mataki na kasa na shugaban matasan jam’iyya a mataki na kwasa, yana kwarewa da sanin ya kamata wannan wa’adin da zai jagoranci jam’iyya reshen jiha muna da tabbacin zai dunke duk wata baraka ko rashin fahimtar da ke tsakanin ‘yayan jam’iyya wanda turbar da ya dauka ke nan a yanzu.

Masu tunani cewar akwai baraka a PDP su fahimci cewar ba mu da baraka a tafiyar mu, domin kan hade ya ke kuma wannan salon da ake tafiya a yanzu itace turba ta dimukuradiyya wanda daman ita PDP malama ce kuma gwana a tafiyar siyasar kasar ne, domin a kullun mu ke kirkiro hanyoyin da za a baiwa jama’a ‘yancin siyasa, mun saba al’adar doki dora a baya, amma yanzu kuma mun shigo da tsarin shugabanci bisa karfin kuri’a, ka ga wannan tafarki ne mai inganci.

Malama Habiba Haruna, shugabar matan jam’iyyar a karamar hukumar Chanchaga cewa tayi, mutane na kallon kamar PDP ta shiga halin rudani akan shugabancin jam’iyya wanda kuma ba haka ba ne, dole a tafiyar siyasa a samu irin wannan turjiyar idan an ce za a kwatanta adalci, domin akwai wadanda sun kasa jure damuwarsu suna fadin maganganu marasa dadi a cikin jama’a, wanda ba mu ji dadin hakan ba.

Amma matakan da ake dauka yanzu bisa jagorancin Baban mu kuma shugaba na riko an fara lalubo bakin zare wanda shi ya kawo tarukan da ake shiryawa tsakanin bangarori kuma mun fara samun maslaha a tsakanin mu. Domin barakar da ake hango mana zuwa yanzu an fara shawo kan ta, da yardar Allah nan da zaben 2023 PDP za ta dawo da martabarta a jihar nan.

Yanzu tarukan da ake shiryawa, tarukan ne na hadin kai da walwale matsalolin da ke tasowa a tsakanin ‘yayan jam’iyya, cikin ikon Allah yau shugabannin mata na kananan hukumomi ashirin da biyar duk mun taru waje daya muna raha kuma ka ga alamar aminci a fuskokin mu, domin mun kwana biyu ba mu ji nunfashin juna ba.

Yanzu wannan zaman ya ba mu damar fahimtar matsalolin da ke damun mu kuma an baiwa kowa damar amaye abinda ke zuciyarsa, hakan tasa zumunci da kaunar juna son jam’iyyar nan ya kara mana azama da fahimtar inda muka dosa.

Kowa ya fahimci cewar irin barin bakan da wasu shugabannin suka dinga yi dan wata damuwa ta kashin kansu yanzu ‘yayan jam’iyya sun fahimci inda suka dosa, kuma ina da yakinin cewar su din ne zasu walwale maganganun su domin PDP ta kowace kuma hadin kai da samar da shugabancin al’umma mai inganci shi ne a gaban dan kafa turbar dimukuradiyya mai inganci a jihar nan.

Dole ne mu dawo, mu dunke waje daya dan sake dunkewa da gaske musamman dan samar da zaman lafiya a cikin PDP wanda shi ne babban kudurin mu kafin babban zaben 2023, wanda turbar maigirma shugaban riko na jam’iyya na kafa harsashen samar da daidaito da hadin kai tsakanin ‘yayan jam’iyya.

Alhaji Garba Umar Chiza zai jagoranci jam’iyya tsawon watanni uku da ake kyautata zaton zai gudanar da babban zaben jam’iyyar na kafa shugabancin jam’iyyar ta hanyar zabe wanda ake sa ran za su jagoranci jam’iyyar tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: