Abdullahi Muhammad Sheka" />

Za Mu Fahimtar Da Alarammomi Game Da Shirin Gwamnatin Kano Kan Makarantun ‘Yan Mari – Goni Laminu

An bayyana shirin da Gwamnatin Jihar Kano, ta kudiri aniyar yin sa na duba halin da Makarantun ‘Yan Mari ke ciki da cewa, wani abu ne mai alfanu wanda ke bukatar kara wayar da kan alarammomi musamman na Majalisar Mahaddata Alkur’ani mai girma a Jihar Kano. Jawabin haka, ya fito ne daga bakin Sakataren tsare-tsare na Majalisar Mahaddata Alkur’ani mai girma ta kasa, Goni Laminu Mahmud Salga, a lokacin da yake jawabi ga taron Mahaddatan Al’kur’ani na mako-mako da aka saba gudanarwa a shelkwatar Majalisar da ke Kano.

Goni Laminu, ya kara da bcewa duba da yadda salon wannan shiri da aka faro daga wasu jihohi da kuma yadda aka aiwatar da tsarin a wasu jihohin. “Babu shakka, mu Majalisar Mahaddata Alkur’ani, mun gamsu da salon gyaran wannan tsari a Jihar Kano, musamman ganin yadda aka samar da matune wadanda suka san ya kamata kuma Ahalin abun. Kamar yadda muka samu labarin yadda Gwamna ya baiwa wadannan ‘Yan kwamitin gudanar da aikin duba halin da wuraren da ake tsare da ‘Yan Marin da kuma irin shawarar da suka baiwa Gwamna, bayan ba su wuka da nama akan aiwatar da shirin da ya yi, babu shakka dole a jinjina musu.

A wasu jihohin, an ga yadda ake yi wa wuraren da ake zargin ana tsare da wadannan ‘Yan Mari dirar mikiya tare da kwashe su zuwa wani wuri, a kuma kamo Malaman da suka mallaki wadannan wurare tare da tuhumarsu, a Jihar Kano ko kadan ba wannan layin Gwamna da masu ba shi shawara suka dauka ba, an baiwa kowa damar sakin wadanda yake tsare da su, domin komawa gidajen iyayensu, wanda daga baya za a zauna tare da duba irin tsarin da ya kamata a yi wa ire-iren wadannan wurare, don inganta rayuwar wadanda ake kokarin kyautata tarbiyarsu.

Salga, ya jinjinawa Shugaban Hukumar Makarantun Allo da na Islamiyya na Jihar Kano, Gwani Yahuzu da Gwani Danzarga, bisa shawarar da a kodayaushe yake baiwa ‘yan’uwa domin inganta harkokin makarantun mu, “wannan kulawa ta Gwani Yahuza ba a kasa kawai ya tsince ta ba, kasancewar a halin tsangaya ne kuma Gwani ne a harkar Alkur’ani, don haka ba ma zaton faruwar wani abu da zai cutar da harkar tsangaya da a halinta matukar ya biyo ta gabansa.”

Saboda haka, sai Gwani Laminu ya bayyana shirin Majalisar Mahaddata Alkur’anin, na fara zagayen Kananan Hukumomin Jihar Kano, lungu da sako domin fadakarwa tare da wayar da kan Alarammomi domin fahimtar da wannan shiri da Gwamnatin Kano ke kokarin aiwatarwa don tsaftace harakar makarantaunmu tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin ana samun fahimtar juna tsakanin wadannan Alarammomi da Gwamnatin Jihar Kano. Ya kuma bayyana
cewa, taron shekara-shekara da Majalisar ta saba shiryawa, a wannan shekara zai mayar da hankali domin kara kyautata danganta da kuma fahimtar cigaban da ake fatan samu a harkar inganta makarantunmu na Allo.

A karshe, Gwani Laminu ya jinjinawa Gwamnatin Kano, bisa fara shigar da makarantun tsangaya cikin shirinta na bayar da ilimi kyauta, wanda a cewarsa a
halin yanzu, akwai makarantun da aka turawa wasu Malamai biyar wasu bakwai domin koyar da hakkokin ilimin zamani da sana’o’i. “Muna jinjinawa Gwamnati bisa wannan kokari, kuma za mu cigaba nunawa gwamnati hanyoyin da ya kamata a taimakawa al’ummarmu, musamman Alarammominmu na tsangaya.

Exit mobile version