Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home TATTAUNAWA

Za Mu Fara Gangamin Wayar Wa Talakawa Kai Kan Zaben 2019 – Kungiyar KYSF

by Tayo Adelaja
September 19, 2017
in TATTAUNAWA
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban kungiyar Katagum Youth Salbation Forum Kwamareda Idris Umar Chinede, ya bayyana cewar, manufar kungiyar ta su itace fadakar da talakawa kan hidimar zabe da kuma zaben wanda ya dace, da bibiyar mene ne zababbun suke tagawa wa talakawansu. Ya bayyana cewa a shirye suke su fara gangamin wayar wa talakawa kai dan gane da zaben da ke tafe. KHALID IDRIS DOYA ya kawo mana tattaunawar kamar haka:

Ko za ka gabatar mana da kanka?

Sunana Comrade Idris Umar Chinade, shugaban kungiyar ‘Katagum Youths Salbation Forum. Ina son yin amfani da wannan dama domin na mikawa mai girma Gwamnan jahar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar Esk, Makama Babba na farko gaisuwa ta musamman domin aiyukan ci gaba da ya ke aiwatarwa a dukkan sassan jahar Bauchi. Allah ya karawa gwamnatinsa kuzari da karsashi domin ci gaba da samarwa jama’ar jaha kayayyakin more rayuwa.

Mece ce tarihin wannan kungiyar taku?

Alhamadu lillahi, ita wannan kungiya mun kirkireta ne tun shekata ta dubu biyu da bakwai (2007). amma bamu samu damar yi mata rajista ba sai shekara ta dubu biyu da goma sha biyar (2015). Kuma wannan kungiya tana bin dukkan sassa na karamar hukumar Katagum domin wayar da kan al’umma game da al’amuran siyasa da kuma al’ummar da suke mulkarmu daga kan Sanata zuwa wakili a majaklisar tarayya, data jaha.

Kamar wasu fannonin siyasa kuke wayar wa jama’a da kai a kansu?

Hakika muna wayar da kan al’umma ne a game da wadanda ya kamata su zaba lokacin zabe na gama-gari da zaben karamar hukuma, kamar ba ni mancewa zaben shekara ta 2015, mun yi iya kokarin mu wajen wayar da kan jama’a akan a yi zabe sak na jam’iyyar APC, kuma Alhamdu-lillahi mun cimma burin mu, an yi wancan zabe sak, kuma an ga nasara a wancan lokaci. Amma abin bakin ciki shi ne daga bisani sai aka samu wasu matsaloli na son zuciya da hassada, da kuma batanci ya shigo cikin al’amarin.

Wannan hassada da batanci sun shigo cikin kungiyar ku ne?

Wato abin da ya faru shi ne, a cikin wadanda muka zaba ne, wasu daga cikin su suke kawo kushe a wasu, kamar misali muna da Sanata guda daya a kasar Katagum, sannan akwai wakili wanda ya ke wakiltar Katagum. Abin takaici shi ne wadannan zababbun ‘yan siyasa sun hada baki, ba kuma su ba kawai, duk Sanatoci guda uku da muke da su a jaha da kuma Wakilai a majalisar tarayya, duk sun hada kai da baki suna kawo kushe da batanci wa mai girma gwamnan jahar Bauchi da gwamnatinsa, kasancewar shi gwamna yana da kokarin kawo ci gaba wa al’ummar jaha, suke amfani da wata dama tasu, suke kawo kushe wa gwamna, sannan kuma su na yin wadansu abubuwa, wadanda muke tunanin hakan ba alheri ban e. Badon komai ba saboda mu muna ganin ba wani abu da suke yi wanda za su bugi kirji, su nunawa al’umma a zahiri abubuwan da suke kawowa mazabunsu, wanda mu kuma a zahirance mun gani mai girma gwamna yana iya kokarin sa wajen kawo ci gaba wa al’ummar jahar Bauchi, musamman hanyar da ya yi mana wacce ta taso daga Misau zuwa Gamawa ta zarce zuwa Zaki. Wannan hanya ce wacce tun lokacin tsohon gwamnan Bauchi, marigayi gwamna Tatari Ali a jumhuriyya ta biyu aka gina ta, kuma ko kwarzane ba a samu wanda ya yi yunkurin gyara ta ba bayan ta sukurkuce, sai shi gwamna Muhammad Abubakar Esk.

Har ila yau akwai wani kwalbati tsakanin garuruwan Misau da Hardawa, wanda kowace damina sai ruwa ya karya kwalbatin, ana yi wa jama’a masu bin wannan haya fito domin haye barakar da karayar gadar ke kawowa, kuma an samu shekaru cikin wannan hali, amma ba wata gwamnati data kawo dauki face ita wannan ta Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, Bauran Katagum, wanda yayi dole a yaba masa.

Kamar wasu irin kushe ne su ‘yan majalisar suke yi wa gwamna da gwamnatinsa. Kuma baka ganin a kan daidai suke yi?

Irin kushen da suke sun hada data matsalar biyan albashin ma’aikatan gwamnati, wanda yanzu haka tunin aka wuce wannan shafin, domin a yau ba gobe ba, ba wani ma’aikacin gwamnati da ya ke bin albashi koda na wata guda ne. Sun yi amfani da wannan dama na cewar su ma wakilai ne na jama’a, bacin cewar sun san halin da kasar take ciki na rashin ingantaccen tattalin arziki a wancan lokaci, amma suka rufe idandunan su, saboda sun ga ire-iren kudurorin mai girma gwamna na ciyar da jahar Bauchi gaba. Kuma ina so jama’a, ba wai na iya yankin Katagum ba, al’ummar jahar Bauchi baki daya da su fahimci wannan, su duba su gani tare da mai da martani a kai musamman ma lokacin zabe mai gabatowa ta shekarar 2019. Kada wasu ‘yan siyasa su zo su yaudare su, su amshe masu kuri’u, kana su tafi su manta da su, domin akwai ‘yan siyasa da su ka iya dadin baki, su yaudare su domin su yarda da su, kuma su yi fatali da su bayan cimma burinsu. Domin idan muka yi la’akari da wasu jahohin tarayya, mu jahar Bauchi ba karamin ci gaba muka samu ba a cikin kankanin lokaci. Idan ka je wasu jahohin, za ka iske ba a ma biyan albashin ma’aikata, ballentana fanshon tsoffin ma’aikata ko garatuti, sa’annan kuma babu aikin yi wa jama’a.

Amma duk da gwamna Abubakar ya zo ya tarar da dimbim basussukan albashin ma’aikata, ga shi kuma gwamnatin da ta shude ba wani abu da ta ajiye a kasa, amma duk da haka, mai girma gwamna ya yi rawar gani, ta hanyar biyan dukkan basussukan albashi da ya samu, ko aka jufga wa gwamnatinsa, ya warware su.

Kamar wasu rawa Gwamnatin M.A ta taka a shekaru biyunta?

Rawar da mai girma gwamna ya taka cikin wadannan shekaru biyu da mulkinsa, ni ganau ne ba jiyau ba, kuma daukacin al’ummar jihar Bauchi ma ganau ne, hakika rawar da ya taka ita ce ya na biyan albashin ma’aikatan gwamnati ba fashi, ba kamar wasu jahohin kasar nan ba, wadanda hakan ta gagara garesu, ya kuma yi matukar kokarin gyara hanyoyi masu yawan gaske da suka lalace a sassan daban-daban na jiha, kuma an gyara makarantun ilimin boko masu yawan gaske cikin wannan lokaci, domin idan ka duba ga misali, tun daga Chinade har ya zuwa Bauchi, na ga makarantu bila-adadin wadanda gwamnatin Barista ta gyara, sa’annan kuma duk inda ka shi ga a cikin jahar nan, lungu-lungu da sako, haka al’amarin yake, ko’ina ana nan ana ta gyare-gyaren su. Bugu da kari akwai asibitoci da aka giggina su a sassa daban-daban na jiha, wannan zage-damtse abin alfahari ne, abin a yaba ne, wannan abin godiya ne wa gwamna, kuma muna masa fatan alheri, Allah ya kaimake shi, damu baki daya, amin

Wace shawara kake da ita wa gwamna, gwamnatinsa ko al’ummar jahar Bauchi?

Shawarar da na ke da ita wa al’ummar jahar Bauchi itace, lalle a yi hattara, mu natsu, musan mene ne siyasa, mu fahimci me ake nufi da siyasa, sa’annan musan wanene ya ke waunarmu, wanene baya kaunarmu, da wanda ya ke son ci gaban mu, da kuma akasin haka, mu cire hassada, mu cire son kai ko zuciya, mu cire kyashi, Insha Allahu za mu cim ma burinmu, zamu cim ma muradunmu. Amma matukar za mu biye wasu wadanda su ba su da buri sai son kansu, ko hassada, to hakika za mu kwan ciki, saboda idan mutum bai fahimci siyasa ba, mutun zai fada tarkon wadanda manufar su itace yaudara da karya da cuta, bayan an zabesu, sun ci zabe, sai su manta da mutum. Ina kuma shawartar gwamnati da ta ci gaba da hakuri, sannan kuma ta ci gaba da jajircewa wajen kawo ci gaba wa al’ummar jahar Bauchi, sannan kuma ta yi kokari wajen wayar wa jama’a kai da fahimtar da su halayen da ake ciki, kasancewa idan ba a samu hakan ba, masu batanci suna samun damar su yi batanci, su yi ta shaci-fadi da zimmar ba ta wani, kana ganin kai farine, sunyi maka fentin baki.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwaman Bauchi Ya Yi Kira Da A Yi Rijistan Katin Zabe

Next Post

Menene Makomar Siyasar Matasa A Kano?

RelatedPosts

Gari

Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari Sun Amince Da Takarar Hon. Yusuf Salihu Shaka -Muntaka Umar Jega

by Muhammad
9 hours ago
0

Editanmu Bello Hamza ya tattauana da Malam Muntaka Umar Jega,...

BIDIYO: Manyan ‘Yan Kasuwar Kano Sun Jinjinawa Dangote Kan Rashin Ƙara Farashi

BIDIYO: Manyan ‘Yan Kasuwar Kano Sun Jinjinawa Dangote Kan Rashin Ƙara Farashi

by Daurawa Daurawa
18 hours ago
0

A cikin wannan hira za a ji yadda manyan 'yan...

NIRSAL

Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Mazauna Abuja, Ya Yabawa Manajan Daraktan NIRSAL

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Mataimakin shugaban yan kasuwar na Arewacin Nijeriya, wato ‘Arewa Traders...

Next Post

Menene Makomar Siyasar Matasa A Kano?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version