Daga Sulaiman Bala Idris, Abuj
Kamfanin NNPC, ya bayyana cewa ya fara bin dukkanin hanyoyin da suka dace domin fara hakar Man fetur a Jihar Sakkwato.
Babban Daraktan Kamfanin na NNPC, Maikanti Baru ne ya bayyana haka yayin da ya amshi bakoncin gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, wanda ya kai ziyarar aiki ga hedikwatar kamfanin da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A wata takarda da mai magana da yawun Gwamna Tambuwal, Imam Imam ya fitar, ya nakalto Babban Daraktan Kamfanin NNPC din na cewa: “Mun jima akan batun fara tunanin hako man fetur a Jihar Sakkwato, kuma an fara bin matakan da suka dace. Mun siyo kayayyakin da ake bukata wadanda da su ne zamu gudanar da wannan aikin.”
Ya kara da cewa tattaunawa ta yi nisa da kamfanin ‘Integrated Data Serbices Limited’ (IDSL) domin basu kwangilan wani bangare na aikin. Wannan, a ta bakinsa, zai sa kamfanin NNPC din ya iya fahimtar ko akwai iskar da ake bakuta a wannan yankin, wanda za ta bayar da damar a gano yanayin man fetur din da ke yankin.
A jawabinsa yayin ziyarar, gwamnan Jihar Sakkwato, Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta gudanar da bincike na musamman dangane da wannan lamarin, wanda kuma za a mika su ga kamfanin NNPC domin ya taimaka musu wurin aikinsu na hakar man da zasu yi.
Ya ce, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar Jami’ar Danfodiyo, za su shirya bita a Sakkwato dangane da yankin da ke da man fetur, wanda za a yi a cikin watan Oktoban shekarar nan, bitar da zata samu halartar masana daga sassa daban-daban na duniya, kuma su gabatar da mukaloli masu muhimmancin gaske.
“Muna gayyatarka da kamfanin NNPC domin ku halarci wannan muhimmin bita, saboda mun yi imanin cewa zai amfanar sosai wurin wayar da kai dangane da hakar mai a yankin na Sakkwato.” In ji Gwamna Tambuwal.