Za Mu Fara Koyar Da Harshen Chana A Jami’ar Ahmadu Bello –Farfesa Adamu

FARFESA ADAMU AHMED Shi ne shugaban cibiyar zaƙulo hanyar samar wa Jami’ar Ahamadu Bello ta Zariya da hanyar ci gaba a ɓangarori daban-daban,  sun jagoranci wasu daga cikin jami’o’in ƙasar nan zuwa ƙasashen waje domin ƙulla zumunci a tsakanin juna, da zaƙulo hanyar da za a bunƙasa ci gaban jami’o’i  na ƙasa baki ɗaya. A dalilin haka ne wakilinmu a Zariya, IDRIS UMAR ya tattauna da shi akan ziyarar tasu, ga yadda hirar ta kasance:

Masu karatu za su so su ji sunanka da matsayinka a wannan cibiyar?

Adamu Ahmed sunana kuma ni ne shugaban shiyyar gano wa da binciken hanyar ci gaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, wato ‘Adɓancement deɓelopment’.

 

Ko zamu iya jin wani irin aiki wannan cibiya taku take gudanarwa a wannan jami’ar da kuma ƙasa baki ɗaya?

Ƙwarai kuwa na farko dai wannan cibiya da nake shugabanta cibiya ce dake kula da hanyoyin da jami’ar za ta samu haɓakar ci gaban aiyukan da ta sa a gaba ta kowane ɓangare. Daga ciki, akwai bincike akan yadda zaa haɓaka nazarce-nazarce da ake gudanarwa, da haɗa kan tsofaffin ɗaliban

don taimakon kai da kai, sai kuma  ƙulla zumunci a tsakanin juna don bunƙasa fasahar da kowa yake da ita, da dai sauransu.

 

Akwanakin baya mun sami labarin kun jagoranci wasu daga cikin jami’o’in ƙasarnan zuwa ƙasashen waje ko zaka iya mana bayanin yadda tafiyar taku ta kasance?

Tabbas a kwanakin baya jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta jagoranci wasu jami’o’i kamar Jami’ar Jihar Adamawa da ta Yobe da dai sauransu bias ga la’akkari da cewa jami’ar Ahmadu Bello Uwa ce ma-bada mama bisa haka ne ta jagoranci sauran jami’o’in ƙarƙashin wata cibiya da ake kira ‘KADUNA ICT HOPE’ wanda shugaban jami’ar ta Ahmadu Bello Farfesa Ibrahim Garba ya ja ragamar sauran jami’o’in ya zuwa wannan tafiyar.

Ita ‘KADUNA ICT HOPE’ cibiya ce dake da rassa a ƙasashe daban-daban ciki har da Amurka, kuma aikin ta shi ne bunƙasa nazarin wani ko wasu tare da ƙoƙarin fito da hanyar da za a ci gajiyar juna bisa haka ne sukashirya wannan tsari, saboda sau da yawa zaka ga jami’o’i sun ƙirƙiri wata fasaha mai ƙyau amma saboda rashin irin wannan zumunci da muke ƙoƙarin kawo wa, kar sai an bar abin ya zama tarihi, to a wannan lokacin shi ne muka ga dole mu tashi tsaye, don mu magance wannan matsalar don haka ne muka ba wannan tsarin muhimmanci tare da aikata shi a aikace.

Daga cikin jami’o’in da muka samu dammar yin tafiyar da su akwai jami’ar Yola da taYobe dadai sauransu kuma mun ziyarci jami’o’in ƙasashe masu yawa, daga cikin wuraren da muka ziyarta ɗin akwai ‘Dura Cell Uniɓersty’ da ‘Teanpule Uniɓersty’ da dai sauransu. kuma abin mamaki shi ne yadda suka karɓe mu hannu biyu kuma bamu baro ziyarar tamu ba sai da shi jagoran tafiyar namu, wato shugaban jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Ibarahim Garba ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin su ‘KADUNA ICT HOPE’ da ƙasashen da muka ziyarta kan cewa, za a ƙarfafa wa juna don haka mun ƙaru sosai don ka san dama an ce tafiya mabuɗin ilmi, to gaskiya mun samo tunanin yadda zamu bunƙasa nazarce-nazarcen da muke dasu don samawa jami’o’in mu ci gaba ta ɓangarori da dama.

 

Farfesa za muso mu ji irin nasarorin da wannan cibiya taku ta samu a shekaru biyun da kasance na shugaban ƙungiyar?

Gaskiya mun sami nasarori masu yawa gaske mussamman in muka dubi halin da jami’o’i suka faɗa na rashin kuɗi, na farko ba zan manta da nasarar da muka samu ba, ta samun tallafin Bankin Duniya na a ƙalla dala miliya4 don ƙarfafa tsarin nazarce-nazarce wannan jami’ar bayan haka, mun yi ƙoƙarin ƙulla zumunci tsakanin dukkanin  ofishin jakadancin dake faɗin ƙasar nan don yanzu haka Chana tuni suka bamu tallafin littatafai masu yawa, tare da ƙulla zumuncin fara koyar da harshen Chana a jami’arAhmadu Bello Zariya bayan haka gidauniyar TY Danjuma tuni su ma suka shigo jami’ar don bada tasu gudummawar idan muka koma ɓangaren jin daɗi da walwala ta ɗalibai tuni Dangote ya dauki alƙawari na gina  ɗakunankwana na ɗalibai guda 10 waɗanda zau ɗauki a ƙalla ɗalibai 2000 kuma akwai wanda suke bada tallafi ga malaman makaranta su tafi waje don ƙara ilmi, ba zan manta da Dakta Dauda Lawal ba na FIRSTBank shi ma ya dawo tsohuwar tsangayarsa, wato cibiyar kimiyyar siyasa ta nan jami’ar. Shi ma ya bada gudummawa ga jami’ar da dai sauran su.

 

To Farfesa duk inda ka ji an sami wasu nasarori sai kaji anyi karo da matsaloli to wani matsaloli wannan cibiyar ke fusakan ta a halin yanzu haka?

Don haka ba zan manta ba, ita kanta ‘Unasko’ ta bayar da shawarar cewar ya kamata ko wace ƙasa ta bada kashi 25 cikin100 daga cikin kasafin kuɗinta, amma a halin yanzu da ƙyar ake samun kashi 5 cikn 100 don akwai lokacin da aka turo miliyan 120 to ka duba nawa ake kashe wa akan wutar lantarki, ka kuma duba ɓangaren sinadarin tace ruwan sha da ake sawa a Dam wanda dole ne a yi, su indai har ana son zaman lafiya?

 

Farfesa wane kira zaka yi ma su tsofaffin ɗaliban da kuke sa rai daga tallafin da za su riƙa ba jami’ar da kuma ita kanta gwamnatintarayya akan halin da jami’o’i suke ciki a halin da ake ciki yanzu?

Ƙwarai muna da kira, kiran kuwa shi ne, gwamnati ta yi ƙoƙari ta duba halin da jami’o’i suke ciki na rashin kuɗi, ga gine-ginen da suke dasu, duk sun tsufa hanyoyin dake cikin jami’o’in duk  sun farfashe, kuma akwai ɗakunan nazarce-nazarcen su, duk suna buƙatar gyara kuma akwai kwasa-kwasan da ake son, kawowa don ci gaban ƙasa amma al’amarin ya ci tura ga haƙƙoƙin Malamai don haka muna kira ga gwamnati da su duba wannanlamarin don kawo gyara. Sai kuma ɓangaren tsofaffin ɗalibai, da muke ƙoƙarin jawo hankalinsu akan bada gudummawa, to su abin da zance masu shi ne, a ƙara ƙaimi domin idan suka lura wannan jami’ar ita ta raine su kuma dole su sata cikin jerin abubuwan da suka ɗaukaka da ransu har suka zama abin da suka zama a halin yanzu, don haka ya kamata duk su zo a haɗa hannu a taimaki jami’ar don ci gaban ilmi a ƙasa baki ɗaya, daga ƙarshe ina miƙa godiya ta gashi shugabn jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba bisa ga iringudummawar da yake bayarwa akan haɓaka ci gaban jama’ar baki ɗaya tare da nuna damuwa akan matsalolin da jami’o’i ke ciki halin da ake ciki a yanzu.

 

Exit mobile version