An ci alwashin farfado da martabar makarantar firamare ta ’ya’yan malaman jami’ar Bayero da ke Kano.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Hon Umar Bala, tsohon dalibi a makarantar da ke Kano kuma wanda shi ne shugaban dalibai a lokaci da su ka kammala ta a 1977, wanda ya bayyana haka a lokacin bikin cika shekaru 50 da kafuwar makarantar, wanda kungiyar tsofaffin daliban makarantar ta BUK Staff Primary School, wato Old Pupils Associations (OLDPA) karkashin shugabancin Dr. Hadiza Galadanci.
Ya ce, “ganin yadda makarantar firamaren ’ya’yan ma’aikata da ke cikin tsohuwar Jami’ar Bayaro ta sukurkuce ta lalace kamar ba wacce mu ka yi ba a 1977 to yanzu ya zame ma na farila wajibinmu mu yunkura wajen inganta ta da dawo da darajarta kamar yadda ta ke a baya koma fiye da haka. Don haka ba tare da daukar wani dogon lokaci ba za mu farfado da darajar firamaran ’ya’yan ma’aikatan BUK da yaddar mai duka.”
Haka zalika Umar Bala ya ce da makarantar na cike da abun sha’awa na shuke-shuke kujeru masu kyau da fenti kwasai kwasi da sauran kayan jan hankali ga dalibai da ka iya bunkasa tinaninsu da kwakwalwarsu wanda ke haifar da yanayi na koyo da koyarwa a wanan makaranta amma yanzu ga shi yadda ta zama dan haka da hadin kan manyanmu irinsu Alhaji Tajjuden Dantata, da shugaban kungiyar tamu da dai sauran manyan yan kauwa da manyan ma’aikata da sauran jama’ar da ke cikin wanan kungiya ta tsofafun dalibai za mu tallafawa wanan makaranta da aka kafata a 1970 kamara yadda ya kamata.