Daga Khalid Idris Doya
Hukumar birnin tarayya Abuja (FCT) ta baiwa bankuna da sauran masu gudanar da harkokin kasuwanci a yankin Maitama da ke Abuja wa’adin kwanaki bakwai da su gaggata tashi tare da yin kaura zuwa cibiyar kasuwanci CBD ko kuma su fuskaci fushin hukumar na garkame wuraren nasu
A cewar hukumar, CBD nan ne aka ware domin ake gudanar da harkokin kasuwanci da sauran lamuran da suka shafi hada-hadar bankuna don haka ne ke kunshe cikin tsarin taswirar birnin tarayyar.
Mai rikon mukamin Darakta a sashin kula da lamuran bunkasa cigaba na hukumar, Garba Kwamkur, shine ya bada wannan jan kunnen lokacin da sashin hukumar suka ziyarci sasannen hanyar Gana da ke Maitama a ranar Talata.
Kwamkur, ya yi bayanin cewa manufar kai wannan ziyarar shine domin tsarkake masu gudanar da kasuwanci tare da tabbatar da masu tafiyar da harkokin bankuna da sauran ‘yan kasuwa sun tafi muhallan gudanar da kasuwanci na asali da aka ware don hakan.
Ya ce, sun baiwa dukkanin masu gudanar da kasuwanci a wuraren da ba a ware su don yin hakan ba musamman bankuna da su gaggauta tashi gami da komawa muhallan asali da suke cibiyar kasuwanci ta CBD ko Idu Industrial Estate wanda nan ne asalin tsarin taswurar FCT ta tsara domin yin kasuwanci da gudanar da harkokin bankuna.
Darakta ya gargadi masu gudanar da kasuwancin da su bi wannan umarnin ko su fuskaci gargamewa daga hukumar da zarar wannan wa’adin sati dayan ya cika ba su bi ba.
Sannan kuma, Mista Kwamkur, ya bayyana cewa, sama a hekta 200 na fili a cikin birnin Abuja mutane sun mamaye ba bisa ka’ida ba wanda suka shiga ba tare da amincewar hukuma ba a yankin Lugbe District.
Kamar yadda ya zayyana ‘yan ta’adda fiye da mutum 150 sun wuce iyaka sun yi gaban kansu inda suka ketara haddin muhallan al’umma a yankin Sabon-Luge.
“Kamar yadda kuke sane hukumar FCT ta yi shelar cewa za a sanya Lugbe cikin gurbin da ya cancanta a tsarin birnin tarayya.
“Don haka tsare-tsaren shigo da yankin cikin tsarin birnin tarayya ya yi nisa.
“Wannan yankin a tsarin zai kasance muhallan tafiyar da harkokin rayuwar jama’a na yau da gobe kamar su makarantu, kasuwanni, asibitoci da sauran wuraren jama’a.
“Wasu kuma har sun fara katsalandar din shiga muhallan da aka ware domin jama’a suna gina gidaje da sauransu. Don haka duk wanda ya ki bada muhallin tamkar ya tauye wa jama’a walwalarsu da jin dadinsu ne,” inji shi.
Wakazalika, Kwamkur ya ce sashin nasu zai aike da sunayen wadanda ake zargi da aikat laifuka ga hukumar ‘yan sanda domi daukan matakan da suka dace na gurfanar da su a gaban kotu daidai da laifukan da ake zarginsu da aikatawa.