Tun a farkon wannan shekarar ta 2020 ne fitaccen Furodusa da ya saba yin finafinan turanci a masana’antar finafinai ta Kannywood Malam Kabiru Musa Jammaje, ya fara gudanar da wani shahararren fim mai suna The right choice, fim din da aka yi wa kasafin kudi wajen Miliyan talatin. To sai dai sakamakon yanayi da aka samu kai a ciki na Cobid-19 hakan ya sa ba a samu damar kammala aikin fim din ba sai a karshen watannan na Nuwamba.
Ganin yadda fim din ya dauki lokaci ba tare da an kammala aikin sa ba da muka irin kudin da aikin ya lashe, wannan ta sa wakilin mu ya nemi jin ta bakin Malam Kabiru Musa Jammaje, ko ya ya aikin fim din ya kasance a cikin wannan yanayi,? Kuma wanne shiri ya ke da shi a yanzu, don ganin jama’a sun fara kallon fim din a cikin kankanen lokacin? In da ya fara da amsa tambayar da cewar.
“To shi wannan fim din namu na The right choice, kamar yadda mutane suka sani, mun fara aikin sa ne a Abuja, kuma daman mun tsara cewar za mu yi mafi yawancin aikin ne a Abuja, wani kuma za mu yi a Kano, kodayakea cikin tsarin ma har da Jigawa, amma daga baya sai muka ga cewar ba sai mun je Jigawa ba, don haka da muka gama da Abuja din sai muka ce mu zo Kano mu karasa. Kuma Alhamdulillahi a Abuja din mun salami dukkan wasu jarumai da muka dakko daga masana’antar finafinai ta Nollywood, don haka mun dawo Kano ne da sinasinai ko goma sha bakwai ne. To kuma mun zo muna kokarin mu karasa, sai kuma Curona ta zo, to kuma ka san yadda Curona ta ke, yadda aka Hana dukkan taruka, don haka sai muka hakura, sai dai a wannan lokacin muka samu damar kammalawa, kuma dai a yanzu Alhamdulillahi mun kammala daukar fim din duka.
Ganin cewar an dauki tsawon lokaci kafin aikin ya kammala, kana ganin hakan bai shafi wani bangare na aikin ba?Musamman ganin cewar ga lokacin da za a kammala ta yiwu ma an saka ranar da za a fara kallon sa?
A can baya kana yin fim ne na Hausa da yaren Ingilishi, kuma dukkan jaruman na masana’antar finafinai ta Kannywood ne, amma a yanzu sai ka hado da ‘yan Kudu wadanda a ke kira da’ yan Nollywood, ko me ya kawo aka samu wannan sauyin?
Wannan haka ne, kuma mun yi hakan ne domin mu jawo hankalin masu kallon finafinan Kudu da ma na Nigeria baki daya, domin ka san Kudu su ne su ke da Sinimomi, kuma sun fi Arewa al’adar kallon fim a Sinimomi, wannan ya sa muka ga ai da dan gari a ke cin gari, don haka sai muka dakko jaruman su, muka hada da namu, sai dai duk labarin kamar yadda na saba yi ne, wato na al’adar Hausa kuma da yawan jaruman na Kannywood ne, kai karewa Ali Nuhu shi ya bada Umarnin fim din. A takaice dai mun yi amfani da wadancan jaruman na su domin jan hankalin su, kamar yadda muka yi amfani da harshen turanci saboda shi ne yaren kasa.
Abin da mutane su ke tamabaya ma shi ne. Wai shi fim din ma me ya kunsa da har ya samu kyakyawan shiri haka?
Shi dai The right choice kamar yadda na ke fada, fim ne da a ke kashe masa makudan kudade har naira miliyan talatin da biyu. Kuma labari ne na wata matashiyar ‘yar jarida da ta ke tsage gaskiya a cikin aikin ta, wanda hakan ya sa ta yi bakin jini a wajen hukumomi, wanda hakan ya sa Gwamnati ta sa aka kama ta, kuma dai daga baya a labarin ya nuna an sake ta. Kuma a tarihin ta, ita Baban ta ya tsani yara mata, shi babanta ya fi son yara maza, sai kuma ya samu mata uka namiji daya, don haka sai ya sangarta namijin saboda so, kuma sai Allah ya daukaka daya daga cikin matan, wadda ta zama ‘yar jarida, bayan kamun da aka yi mata daga baya sai ta samu matsayi mai girma. To wannan shi ne labarin fim din a takaice, amma dai sakon da ya ke ciki sai wanda ya kalla ne zai iya gani.
Ganin cewar yanzu kasuwancin fim ya mutu sai dai a kai shi Sinima, ko akwai wani tsari da ka yi na yadda kudaden da ka kashe za su dawo?
To gaskiya da yardar Allah, tun da muna ganin labari ne da muka yi mai kyau, muna fatan zai ja hankalin mutane a nan kasa Nigeria da ma duniya baki daya. Kuma ka san wannan shi ne fim na farko daga Arewa da aka kashe masa kudi, don haka lokacin da fim din ya fito muna fatan jama’ar Kasa baki daya kudu da Arewa za su fito don su kalla su ga me muka zo da shi, kuma wannan me suka zo da shi din in sha Allah, shi ne zai jawo mana yawan masu kallo, yadda zai zama an samu damar da za a mayar da kudin da aka kashe, kuma har ma a ci riba. Kuma akwai a Internet, wannan Dandalin da a ke kallon finafinai na Netflid, shi ma muna sa ran hankalin su zai dawo kan fim din, yadda idan hakan ta faru, sai dai mu yi Sambarka.
To akwai tsarin za a haska shi a Sinimomi na waje?
To a bangaren You Tube fa da a ke yayin saka finafinan mu na Kannywood?
A gaskiya wannan ba fim din You Tube ba ne, sai dai a saka wani yanki a cikin You Tube din domin talla.
Daga karshe wanne kira za ka yi ga al’umma dangane da fitowar fim din The right choice?
To kiran da zan yi shi ne idan fim ya fito mutane su nuna kishi su fito su kalla. A duk in da su ke a Kasar nan musamman ma dai a Arewacin Nigeria, daman labarin na Arewa ne, su ‘yan kudu da muka saka mun saka su ne don mu ja hankalin masu kallon su saboda kasuwanci, don haka jama’a su ba da hadin kai wajen kallon fim din The right choice muna fatan za mu mayar da kudin aikin da muka yi har mu ci riba, kuma da yardar Allah ba za mu ji kunya ba.
To madalla mun gode.
Nima nagode Sosai.