Za Mu Horas Da Manyan Jami’ai A Sauran Fannin Aikin Soja, Inji Kakakin Rundunar

Mazauna Kauye

Rundunar sojin Nijeriya ta 81 dake garin Legas, ta bayyana shirinta na horas da manyan jami’an sojin Nijeriya a fannonin ayyukan soja da ba yaki ba, wannan horan zai takaita ne kawai ga manyan jami’ai da suke a Legas da jihar Ogun.

Mai magana da yawun runduna ta 81, Laftanar Kanal Olaolu Daudae, an tsara wannan horaswar ne don karawa manyan jami’an dabarun ayyukan soja, da kuma karar horar da manyan kwamandojin rundunar a daidaikun su da kuma  a hadensu a matsayin runduna.

Wannan horaswar za ta karawa jami’an kwarewa a fannin gudanar da ayyukansu, sannan zasu kara samun gogewa a sauran fannonin aikin soja da ba na yaki ba.

Exit mobile version