Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, Rumelu Lukaku, ya bayyana cewa yana ganin har yanzu suna da damar lashe gasar cin kofin Siriya A ta bana saboda akwai ragowar wasanni da dama a nan gaba.
Romelu Lukaku ya saka wata kwallo a raga da ka a karin lokaci a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin kalubalen Italiya a karawa tsakanin kungiyarsa Inter Milan da Fiorentina da aka tashi 2-1 a daren Laraba, lamarin da ya sa yanzu za su kara da AC Milan a zagayen kungiyoyi 16.
A minti na 119 Lukaku, dan kasar Belgium ya yi amfani da kwallon da Nicolo Barella ya kawo masa daga kusurwa, inda ya saka mata kai har ta wuce mai tsaron ragar Fiorentina Pietro Terracciano.
Tun da farko dan wasa Arturo Bidal, dan kasar Chile ne ya ci wa Inter Milan kwallo ana saura minti 5 a tafi hutun rabin lokaci Christian Kouame ya farke minti 12 bayan an dawo hutu, abin da kenan ya kai wasan karin lokaci.
Bayan an tashi daga wasan ne Lukaku ya bayyanawa manema labarai cewa har yanzu akwai ragowar wasanni a kakar wasa ta bana saboda haka komai zai iya faruwa nan gana kuma suna da damar lashe gasar Siriya A ta bana da ake bugawa.