Abba Ibrahim Wada" />

Za Mu Iya Lashe Kofuna Hudu A Wannan Kakar – Guardiola

Guardiola

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce abin alfahari ne ya zamana kungiyar ta yi nasarar lashe kofuna har 4 cikin kaka guda dai dai lokacin da kungiyar takai wasan warshe na cin kofin Karabao Cup.
Manchester City dai ita ce kungiya daya tilo da ta ke da zarafin iya lashe kofunan Firimiya da FA da kofin League da kuma zakarun Turai la’akari da matakin da ta ke a kowacce gasa kuma kungiyar tanada karfi.
Yanzu haka dai Manchester City na da tazarar maki 4 ne kacal tsakaninta da Liverpool da ke saman Teburi, a bangare guda kuma anga rawar da ta ke takawa a gasar ta FA da ma yadda ta ke shirin tunkarar wasan karshe a gasar League tsakaninta da Chelsea cikin watan Fabarairu baya ga gasar zakarun Turai.
“Abu ne mai wahala lashe kofuna hudu a duniya musamman a kasar Ingila amma kuma abune wanda zai iya kasancewa saboda haka muma a matsayinmu na kungiya mai karfi zamu gwada yin hakan” in ji Guardiola
Yaci gaba da cewa “Gasar cin kofin Karabao munzo wasan karshe sannan kuma gasar firimiya itama muna matsayi na biyu kuma zamu iya komawa mataki na farko nan gaba kadan idan muka cigaba da samun nasara a wasannin mu”
Kawo yanzu dai Manchester City ce kungiya ta farko a kasar Ingila da take buga gasar cin kofin zakarun turai da gasar cin kofin Karabao da kuma kofin kalubale da kuma gasar firimiya duka a wannan akkar.

Exit mobile version