Abba Ibrahim Wada" />

Za Mu Iya Lashe Laligar Bana, In Ji Zidane

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa yana ganin kungiyarsa zata iya lashe gasar laliga ta bana bayan daya jagoranci kungiyar ta lashe wasa da kungiyar Osasuna a ranar Larabar data gabata.
Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga na bana, bayan da ta doke Osasuna da ci 2-0 a wasan mako na shida da suka fafata a filin wasa na Santiago Bernabeu ranar Laraba duk da cewa sunsha wahala a fafatawar.
Hakan ya sa har yanzu Real Madrid ba ta yi rashin nasara ba a kakar La Liga ta shekarar nan, inda ta ci fafatawa hudu da canjaras biyu, ta kuma ci kwallo 12 aka zura mata guda shida a raga kawo yanzu.
Kociyan kungiyar, Zinedine Zidane, ya ajiye wasu manyan ‘yan wasansa da ya hada da Gareth Bale a shirin da yake na fafatawa da Athletico Madrid a wasan gaba na La Liga da zai fuskanta kuma wasan hamayya ne.
“Ina ganin kamar zamu iya lashe gasar laligar bana idan muka duba irin nasarar da muke samu kuma abokan hamayyarmu basa cikin yanayi mai kyau saboda haka akwai bukatar mu cigaba da dagewa idan har munason hakan ta tabbata’ in ji Zidane
Osasuna ta saka kwazo sosai, sai dai Real ta zura kwallon farko ta hannun binicius Junior, kuma kwallo ta farko da ya ci wa kungiyar a kakar bana sannan Real Madrid ta kara kwallo ta biyu ne ta hannun Rodrygo da hakan ya ba ta maki ukun da take bukata a wasan.
Real ta koma ta daya a kan teburi da maki 14, bayan cin wasa hudu da canjaras biyu, za kuma ta ziyarci Atletico Madrid a wasan mako na bakwai a gasar ta La Liga ranar 28 ga watan Satumba a wani wasa mai wahala kamar yadda Zidane ya bayyana.

Exit mobile version