Abba Ibrahim Wada">

Za Mu Iya Sake Lashe Gasar Firimiya, Cewar Sabon Dan Wasan Liverpool

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Diogo Jota, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa kungiyarsa zata iya sake lashe gasar firimiya wadda aka fara a satin daya gabata saboda yadda suke da karfin yin hakan.

Kungiyar kwallon kafar ta Liverpool ta amince ta sayi dan wasan gaban na Wolbes Diogo Jota a kan yarjejeniyar da za ta kai fam miliyan 45 idan aka hada da ‘yan tsarabe-tsarabe kamar yadda kungiyar ta tabbatar a shafinta.

Kungiyar ta dauki matakin sayen dan wasan Portugal din ne mai shekara 23 bayan Liverpool ta sayi dan wasan kasar Sipaniya, Thiago Alcantara daga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich akan kudi fam miliyan 25.

Advertisements

A wata yarjejeniayr ta daban, Wolbes na shirin sayo dan wasan Netherlands mai shekara 18 Ki-Jana Hoeber daga Liverpool kuma ana sa ran Wolbes za ta biya fam miliyan 9 kan Hoeber, kodayake akwai yiwuwar kara masa £4.5m na alawus-alwus da kuma kashi 15 na kudin darajar dan kwallo.

Jota ya je Wolbes a kakar wasa ta 2017 zuwa 2018 a matsayin aro, amma daga baya ta saye shi a kan fam miliyan 12.8 a shekarar 2018 kuma ya buga wasa sau 131, inda ya zura kwallo 44, ciki har da kwallo uku-uku a wasa daya na gasar Europa inda suka doke Besiktas da Espanyol.

Jota zai zama dan wasa na uku da Liverpool ta saya a bazarar bayan Alcantara kan £20m da kuma dan wasan Girka Kostas Tsimikas a kan £11.7m a kokarin da kungiyar ta keyi na ganin ta kare kambunta na gasar firimiyar Bana.

Exit mobile version