Za Mu Iya Samun Nasara Ba Tare Da Messi Ba – Koeman

Duk da rashin Messi sakamakon horon dakatarwa na wasanni biyu da hukumomi suka ba shi, Barcelona sun doke kungiyar kwallon kafa ta Elche da ke samun matsaloli a gasar La ligar Sipaniya har gida da ci 2-0 a yammacin Lahadi, kwallayen da Frenkie de jong da Rikui Puig suka ci.

A minti na 39 ne Barcelona ta ci kwallo ta farko, kwallon da ta yi kama da Elche sun ci gida ta hannun Diego Gonzales, amma De Jong, wanda shi ya kawo kwallon daga kusurwa ya yi wuf ya taba ta kafin ta shiga raga.

Dan wasan gefe na Elche Emiliano Rigoni ya barar da damar farke kwallon da aka saka mu su a raga bayan wani kuskure da mai tsaro bayan Barcelona Oscar Mingueza ya tafka, amma mai tsaron ragar Barcelona, Marc-Andre ter Stegen, ya hana shi kaiwa ga gaci.

Barcelona sun yunkuro a minti 89, inda suka kara kwallo ta biyu ta hannun Puig, wanda ya sa wa wata kwallon da De Jong ya kawo kai, abin da ya ba su nasara 4 a jere kuma kawo yanzu  Barcelona tana matsayi na uku a teburin La Ligar Sipaniya da maki 37 a bayan masu jan ragamar gasar, Atletico Madrid, wadanda suka ba su ratar maki 7.

Bayan tashi daga wasan ne mai koyar da ‘yan wasan Barcelona, Mista Roland Koeman, ya bayyana cewa duk da rashin babban dan wasa kuma kaftin, Leonel Messi, kungiyarsa zata iya samun nasara a wasanni kuma yana fatan zasu dora daga inda suka tsaya domin ganin sun kai inda suke so.

Exit mobile version