Bello Hamza">

Za Mu Kafa Kamfanin Samar Da Bulawus Na Farko A Fadin Afrika—Ambasada Dayyabu Sa’ad

Editanmu Bello Hamza ya tattauna da Ambasada Dayyabu Sa’ad shugaban kungiyar masu sana’ar sayar da Bulawu na jihar Kano a kan kalubalen da kungiyar ke fuskanta da kuma irin shirye shiryen da suke yi don bunkaa kungiyar, ga dai yadda hirar ta kasance

Zamu so ka yi mana bayani kan taron ku da kuka so yi na shugabannin kungiyar wanda kuma ya samu tangarda da kuma halin da ake ciki.

To da farko dai ni sunana Ambasada Dayyabu Sa’ad Shugaban Kungiyar Masu Sayar Da Bulawus na jihar Kano, Kuma acting chairman na Arewacin Nijeriya. Yawwa dalilin haduwar mu a Kaduna shine gudanar da taro da muka saba yi na annual general meeting. Wannan dai shine taro na uku na kungiyar. Na farko muyi shi a Bauchi Azare na shekarar da ta wuce mun gabatar da shi a jihar Kano to wannan shine muka gabatar dshi a Kaduna duk da dai akwai tangarda da muka gamu dashi a cikin taron, Amma dai da yardar Allah abun da muka so much gabatar din mun samu mun yi nasarar gabatar da wasu daga ciki. Kuma dalilin haduwar mu a wannan taro ma dai na bana shine akwai yinkurin da muke yo na samar da babbar kanfani a Arewacin Nijeriya wanda zai rika samar da kayayyaki na yara.

Wanda yake kafin nan ana shigo dasu daga kudanci kenan?

Na farko da musamman majority a nan jihar Kano, muna siyan kaya dga ksasje irin Chana, India, Dubai, da sauransu, harma wani bangare na sashin Thailand. To Kuma a Nijeriya mu kaman daga Nan jihar Kano da kuma sauran jihohin Arewa, a na shiga irin garin Onacha da Legas Ana siyo ireiren wadannan kayayyaki. Na cikin gida kenan sabanin wancan da zamu yi order daga waje. To kuma saboda yanayin kullum yadda zamani yake canza da juyawa da kuma kullum an kokarin updating na rayuwa da abubuwa, shine babbar kungiyar ta Arewa wanda nine shugaban riko muka yi tunanin lallai mu samar da babbar kanfani na samar da wannan kayayyakin a Arewacin Nijeriya. To Kuma duk zaman da muka yi na bara da na bana akan wannan kudurin ne. Musamman ma bana saboda wasu nasarori da muka kara samu, shi da muka zo maganan gabatar da taron da kuma sauran jihohi mu sanar dasu na farko muna so a samar da wannan babbar kanfani anan jihar Kano wanda zai rika samar da kayayyakin yara koda za a siyo wasu daga wake ya zamanto akwai Wanda muma a nan Nijeriya muke samarwa. To shine makasudin wannan taro. Agendan mu na biyu akan wannan taro shine samar da wata takarda kwaya daya wanda zai zamanto mun yi anfani da shi a duk Arewacin Nijeriya duk inda zaka ka lodo irin wannan kaya na bulawaus ya zamanto akwai wanda za su duba su san abun da ka dauko, bulawus din ne ko kayan want abu sabanin wanda doka bata so saboda zirga zirga a cikin kasa. A hada wasu kayan da wanda ba daidai ba. To shine a dlilin zaman namu zamu samar da takatda in a Kano zaka zo ka dauki wannan kaya daga nan ka tafi wasu jihohi. Maiduguri, Admawa, da sauransu. To ya zamanto wannan kungiyar ta san lallai dole a motan da aka dauka kayan ka ne na bulawus wanda gwamnatin Nijeriya ta yarda ko a shigo da su ko ayi yawo dasu a cikin kasa a saida. To in kuma daga kudanci Nijeriya kaje ka siyo, Legas ne ko Anacha. Za a aje wakilin da zai baka wanna takarda da zai tabbatar abun da ka fada din shine. Wannan shine daliln, zaman mu na biyu na kuma na samar da wannan takarda kwaya daya duk inda zaka dauki ire iren kayan mu ka yi yawo dasu a Nijeriya ka tafi a mota kaje wata jihar ka saida sai an tabbatar kayan ne saboda tsaro musamman ma da yanzu kayan laifufuka suka yi yawa shine kusan wannan abun biyu da ya zaunar damu a Kaduna.

Kuma aka samu nasarar gabatar da wasu abubuwa da dama. Bayan mun tashi daga taro muka sake dorawa a masaukinmu zuwa washe gari wanda kusan misalin karfe tara ko wace jiha Kuma ta nufi gida. Kuma Kamar ‘yar matsalan da ta shigo daga ciki shine na sabanin wasu jihohi da muka dan samu ya zo basu aminta da shugabancin wasu daga jihar ba, wasu jihohin kuma an sa samu shugabancin biyu. Shine kungiyar mu take kokarin taga kowace jiha ta yi anfani ta bamu shugabanci kwaya daya.  Shine zai bamu nasarar da zamu cinma abin da muke so muyi, Saboda wanna kayan da muke so mu samar da wannan kanfani, muna so ya zama kowace jiha tana da kayan da za a murza mata, wanda wannan kayanta ne jihar za’a kai. Kaga kenan kanfanin zai tafi da wuri, zai samu kudin shiga da wuri ya zamanto kowace jiha tana da wani kaso a cikin wannan kanfanin da zamu samar. Ya zamato akwai wannan kayan su wannan na jiha kaza ce wannan na jiha kaza ce, mutum zai iya zuwa ya siya wasu jihohi Amma a karkashin kungiyar zamu yi tsari.

 

Ta ina kuke sa ran samun kudaden gudanar da wannan kanfanin

Toh gaskiyar magana akwai wasu adadi da muke so su fita daga cikinmu ‘yan kasuwa, kuma akwai wanda muke so mu yi a kudurce mu nema daga Gwamnati na karin karfin gwiwa. Muna so ya zamo kamfani ne wanda zai taimaki al’umma da kuma aasa da Arewacin Nijeriya baki daya. Muna da wannan kuduri, saboda sai da dama wasu abubuwan da zamu je mu siyo, kasan fita zamu yi kasashen waje mu siyo injinanan da zamu kafa a wannan kanfanin. Kanfanin zai ci wajen Biliyan Uku da wani abu muke tunanin abin da za a fara samarwa a wannan kanfanin zai kai Naira Biliyan Uku da wani Abu. Toh dole akwai adadin wasu kudade wanda mun yi nisa wajen samar dasu ta wannan jihohi. To Kuma akansu akwai wanda mukes on zammu nema ta gwamnatin tarayya da ta sa hannu a cikin samar da wannan kanfanin.

Zuwa yanzu akwai wani nasara da aka samu na neman hadin kan Gwamnati ga wannan kudurin naku?

Gaskiya ne mun fara ‘processing’ din abubuwa da dama duk da a yanzu akwai inda muke so kanfanin nan ya tabbata misali gurin da za a samar da shi. Na samun yanayin ginin da ya dace, da wurin da ta dace a samar da shi to wannan mun yi nisa kuma akwai rubuce rubuce da wasu ka’idoji da muke son tsarawa kusan a dai nan da wata biyu muke son mu yi babbar zama da wasu bangare na wakilan Gwamnati.

Wani kira kake dashi ga mambobin kungiyar na a kwantar da hankali a hada Kai don a samu cikakkiyar nasara musamman ganin dan hargitsin ko ince yamutsin da aka samu a taron Kaduna.

Gaskiya ne abun da muka kara gaya musu ko a ranar bayan kowa ya sauka muka nuna musu cewa duk harkar arziki bata yiwuwa da tsiya arziki da tsiya basa haduwa a wuri daya. Kuma duk abin da akwai nasara cikin sa dama akwai irin wannan ba komai bane zai taho da nasara ya zamanto cikin kwanciyar hankali indai abu ne ana ganin da nasara a cikin sa, farko dole akwai jarabawa da zaku samu, amma in kuka yi hakuri zaku dinke duk wani da zai iya faruwa a gaba kuma hakan ma yasa muka cimma nasara a garin duk wasu suka yafi juna aka yi maganganu mai kyau muka yi tsari mai kyau. Yanzu haka taron shekara mai zuwa nan da wasu ‘yan watanni muna son zamu yi a jihar Sokoto ne. Muna so mu yi wannan tasrin amma da dama yanzu duk wasu rubuce rubuce da muka yi jihohi sun karba tun anan gurin sulhu da juna an yafi juna komai ya wuce wannan abin da muke so mu cimmma bazai yiwu ba saboda haka dole sai an da shine shugaba a jiha kaza kungiyar. In muka samu wannan hadin kai shi zai tabbatar mana da babbar nasara akan wannan kudurin da muke da shi kuma wannan abubuwan da muka tattauna a Kaduna gaskiya mun cimmma nasara.

A cikin wannan nasara da kake maganan an samu dole akwai wasu wandanda suka jajirce kuma watakila zaka so ka mika godiya a gare su a cikin wanna tafiyar?

Musamman sakataren wannan kungiyar Alhaji Abubakar daga Jos ya taka rawa mai mahimmanci sosai wajen fahimtar da jama’a inda muka dosa. Kuma akwai ‘Oorganizing Sectetary’e na wannan kungiya, Alhaji Yakubu Muhammad daga jihar Niger ya yi kokari sosai sai mataimakina anan Kaduna. A takiace shima Dan Jummai da nake yi nake magana shi ne mataimakina na wannan kungiya a nan Kaduna to gaskiya ya yi kokari sosai kuma musamman mutanen nan you akwai shi jajirtaccen mutum wanda Shima ya tsaya tsayin daka shi ne ‘Chairman’ na wannan kungiya a nan Kano muke tare da shi don yana kokarin yada duk abubuwa akan lokaci to musamman dai wannan da muka hada gaskiya suna bani hadin kai wajen tafiyar da wannan kungiya.

Ranka ya dade Mun gode

Nima na gode

Exit mobile version