Connect with us

SIYASA

Za Mu Kafa Kungiya Domin Fidda Shugabani Na Kwarai (I) -Rimin Zayam

Published

on

BASHIR BUKAR RIMIN ZAMAN daya ne daga cikin dattawa a hidimar siyasa, kuma ya kasance masani sosai kan hidimar siyasar kasar nan, haka kuma Tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP na jihar Bauchi. a hirarsa da LEADERSHIP A Yau, ya bayyana cewar yanzu haka suna kan shirye-shiryen kafa wata kungiyar da za ta maida hankali wajen kokarin ganin jama’a suna zaban dan takarar day a dace a maimakon maida hankula kan jam’iyya gaba daya. Ya ce, Mutum shi ne ake zaba ba jam’iyyarsa ba, halin kwarai na mutum da kuma irin burinsa na kawo ci gaba ne abun maid a hankali ba wai a wace jam’iyya ne mutum ya fito ba. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi kamar haka:

Ka gabatar mana da kanka mana?

Suna na Alhaji Bashir Bukar Rimin-Zayam ni dan siyasa ne kuma dan jam’iyyar PDP, ina kuma daga cikin wadanda su ka yi hidima wajen kafa jam’iyar.

Me za ka iya cewa kan zaben 2019 da ke tafe?

Siyasar da za ta zo 2019 a yanzu ma muna kokarin kafa kungiya, wannan kungiyar da muke kokarin kafa shi ne za a yi amfani da waje kai? mene ne ka yi jiya? idan ka taba rike wata matsayi. Mene ne ka yi a lokacin da ka rike wani mukami, kama daga na zabe ne ko kuma wanda aka nadaka. Wani irin gudunmawa ka kawo wa jihar, kasar da karamar hukumarka, meye shekarunka? Kuma yaya ne ka damu da mutanenka da damuwarka wa kasar nan. sannan ka damu da kasar taka ma kuwa. Shi ya sa yanzu za ka ga da yawan mutane za su koma bayan za a yi mutum ne ba jam’iyya ba.

Kamar ya mutum ba jam’iyya ba?

Eh mana, jam’iyyun nan gaba daya babu Kur’ani balle Hadisi, babu Kur’ani babu kuma Baibul, kowani wanda ka ganshi a cikin siyasa yana yi ne domin kasarsa da aljihunsa, don haka ne mutane ya kamata ne su nutsu kada su ruga da gudu, su ce yau in jam’iyya ‘A’ ne sai su ruga da gudu su ce jam’iyya ‘A’ za su yi sama da kasa. Idan jam’iyya ‘B’ ne su ce ita za su yi sama da kasa, haka idan ‘C’ su ce sama da kasa.

A’a, a tsaye na duba wadanda suka dace, wadanda za su kawo ci gaba wa kasa, jiha da sauran kujeru. Domin wani shi zai zabi gwamna a jam’iyya kaza amma ba zai zabi sanatan da ke jam’iyyar su wane ba, wani kuma zai zabi sanata amma ba zai zabi gwamnan da ke jam’iyyar su sanata wane ba. Za ka samu daga kan gwamna, zuwa shugaban kasa zuwa dan majalisar tarayya zuwa dan majalisar dokokin jiha, wani za ka samu dukkanin wadannan kujerun jam’iyyun daban-daban wani zai yi. Mene ne dalilinsa? Saboda a ganinsa cancantar mutum da mutuncin mutum. Saboa mun shiga wani irin yanayi na siyasar da ake ciki. Wadansu zababbu sun ci amanar jama’arsu, kasarsu, sun kuma ci amanar jam’iyyarsu da kuma cin amanar shugabansu.

Mu a wajenmu cin amanar dan siyasa shine a zabeka ka tafi ba za ka zo mazabarka ba, ba za ka zo karamar hukumar ka ba, ba za ka zo wajen al’ummarka ba, ba za ka zo ka nemi shawararsu ba, idan za ka kawo wani abu ba za ka zo ka nemi shawararsu ba, balle su tsaya su yi addu’a kan cewa za a kawo musu kaza da kaza, sai dai su ci gaba da fada da abokan jam’iyyarsu ko kuma da ‘ya’yan jam’iyyarsu, wannan babbar asarace a jiha, idan haka ta auku. A bisa wannan dalilin ne za mu kafa kungiya mai sunan ‘waye ya dace’, idan kana da jam’iyya mai suna ‘A’ kowaye kai jama’a za su iya zabenka koda basu sanka ba, idan kana jam’iyya ‘B’ ko ba kasan mutanen ba ko sun sanka saboda ganin cewar ka yi abun da ka yi na kwarai za su zabeka.

Yanzu misali kwanan nan abun da ya faru da mu na rasuwar Ali Wakili, da yawan mutane basu san waye Ali Wakili ba, me zai iya yi mai zai yi ba sai da bayan lokacin da ya rasu ne jama’a suka san waye shi. Irin wadannan abubuwan ne fa ya kamata jama’a suke zabowa, yanzu misali zaben da za a yi na Sanatan nan dole ne mutane su nutsu su zabi mutum da ake cewa nagartacce, su duba waye mutum, wani irin gudunmawa ya taba takawa, wani mukami ya taba rikewa, a jaha ne, karamar hukuma ne a kasa ne ko a wata kasa, jama’a sai su duba su binciko a lokacin da ya rike wannan mukamin mene ne ya iya samarwa na ci gaba. Don haka sai jama’a su zabe sa a bisa hakan. Hakkin zaben nagartacce na wuyan talakawa.

Mene ne ya sanya kake damuwa sosai kan hakan ne kam?

Yanzu kamar abun da ke faruwa a nan jihar Bauchi sai ka ga mutum ya sayi amsakuwa (lasifika) na massalaci sai ya je ya ce maka ya kawo ci gaba wa jama’a, har ma ka ji ya ce maka Sadakatujjariya ne, ko ka ga wani ya kawo kafet din massalaci sai ya ce maka ya kawo ci gaba, ko kuma sai wani dan siyasa ya je asibiti ya dauki dubu 2 biyu yana raba wa marasa lafiya sai a ce ya kawo ci gaba, ta ina ne ci gaba a nan? ci gaba a siyasance ka kawo hanya a garinku, ka hada kan kasarka ka kuma yi kokari ka taimaki jama’an da suka kawo ka ba, ka dauki dubu 50 ko 30 ka ce ka taimakesa ba, a’a ka yi masa hanya shi ma ya tsaya da kafafunsa.

Yanzu abun da ke neman ya samemu, tun lokacin da aka kafa majalisu akwai maganar kan iyaka, idan kuka dauki wani shashasha kuka tura majalisa wanda bai san mene ne matsalar kasar nan ba, bai san kuma ina ne ma kasar nan ta sanya a gaba ba, mene ne matsalar Arewa, mene ne matsalar da ke gaban Arewa, dukkani wani dan siyasar bai ma san wadannan matsalolin ba, amma jama’a za su turasa majalisa, dole jama’a su tsaya su duba wannan lamarin.
Advertisement

labarai