Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Zababben shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Hassan Garban Kauye Farawa ya bayyana aniyarsa na mayar da hankali tare da bada fifiko wajen unganta rayuwa da habaka tattalin arzikin al’ummar Karamar Hukumar Kumbotso ne abinda zai mayar da hankali, shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP Ayau a Kano.
Farawa ya ci gaba da cewa, dole mu duba kamfanonin da ke wannan karamar hukuma domin tabbatar da ganin cewa al’ummar wannan karamar hukuma sun cika gurbin da doka ta yi tanadi ga duk yankin da kamfani ke gudanar da harkokinsa, haka kuma akwai bukatar inganta hanyoyin samun karin kudaden shiga domin ci gaba aiwatar da kyakkyawan munufofin wannan Gwamnati.
Da yake tsokaci kan yadda zai tunkari wasu daga cikin kalubalen dake gabansa, musamman batun sake dawo da darajar shugabancin Karamar Hukumar da abaya ake yiwa wani irin kallo, Alhaji Garba Kauye Farawa yace zamu tabbatar da yin koyi da kyawawan munufofin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma jagororinmu a Karamar Hukumar Kumbotso, wadanda kullum cigaban al’ummar Kumbotso ne a gabansu.
Alhaji Garban kauye Farawa ya bukaci Abokan aikinsa Kansiloli da ja damara tare da sadaukar dakai wajen gudanar da ayyukansu bil-hakki da gaskiya, Haka Kuma ya bukaci hadin Kan iyayen Kasa da malaamai domin Samar da ingataccen ci gaban da ake bukata.