Connect with us

LABARAI

Za Mu Kashe Naira Biliyan 13 Don Yin Feshin Kwari A Arewa, Inji Minista

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yarda da kashe Naira biliyan Sha uku N13bn don yaki da kwari (fari) a jihohi sha biyu na Arewa.
Jihohin sun hada da: Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Yobe da Borno.
Alhaji Muhammad Nanono, Ministan Gona Da Raya Kauyuka, ya bayyana hakan a wata sanarwa da yafitar a ranar Asabar, yace kudin an bada sune don rage radadin korona data nemi kassara tarin abincin Tarayyar Nijeriya.
Acewar Ministan, an ware wannan kudin ne don gudun duk wani abu daka’iya kawo cikas a noman wannan shekarar ta 2020 a wadannan jihohin.
Ya kara da cewa, kudaden za ayi amfani dasune wajen dakile barazanar kwari dake shigowa daga kasashen makobta, kuma sannan a rage radadin Barnar korona, kuma a tara abinci don lafiyar kasa.
Ministan ya kara jaddada cewa, wannan gwamnatin zatayi duk abinda yadace tayi akan taga ansamu nasarori akan harkar noma kuma ta dakile duk wata barazana dake nufo harkar gona.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: