Khalid Idris Doya" />

Za Mu Kwato Kujerarmu A Kotu, in ji Gwamnan Jihar Bauchi

• A Shirye Muke Mu Hadu Da APC A Kotu, in ji PDP

Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya sanar da cewar yanzu haka uwar jam’iyyar APC ta kammala shirye-shiryen tafiya kotu a karo na biyu domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi da ya kai ga samar da dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir a matsayin sabon gwamnan jihar.
Gwamna Abubakar, wanda ke shaida hakan a lokacin da magoya bayansa suka hallara domin taya shi murnar dawowa daga rakiyar shugaban kasa Buhari zuwa kasar Senegal a ranar Laraba, yana mai shaida cewar ya tafi Abuja ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a APC, inda ya shaida cewar dukkanin iyayen jam’iyyar a matakin kasa sun tabbatar masa da cewar za su je kotu domin kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar.
Ya shaida cewar a matsayinsa na mai biyayya ga jam’iyyar APC ta kasa, ba zai bijire wa matakin da jam’iyyar ta dauka ba, domin tun a farko da bazarta ya taka rawa, yana mai shaida cewar APC ta dauki manyan lauyoyi masu mukamin SAN har guda hudu da za su kasa-su-tsare a kotu domin amso wa APC hakkinta a kotu kan zaben gwamnan jihar.
A ta bakin gwamna M.A, “Dalilina na tafiya zuwa Abuja, a matsayina na dan jam’iyya mai biyayya na je na sadu da shugaban jam’iyya na kasa baki daya, na sadu da mataimakin shugaban kasa, na sadu da shugaban kasar Nijeriya. Kamar yadda na fada ni mai biyayye ne ga uwar jam’iyya ne. a dalilin haka ne dukkanin wurare ukun nan da na je kowannensu abun da ya ce shine jam’iyyar APC za ta shigar da kara akan zaben gwamnan jihar Bauchi.
“To, ni kuma a matsayina na mai biyayya ga jam’iyya na amsa zan bi matakin da ta dauka. kowa ya sani lokacin da aka fadi sakamakon zabe tawakkali na yi; amma kuma, gaba ma da gabanta uwar jam’iyya da ita ce na yi rawa, ta ce ita bata yarda ba za ta shigar da kara,” A cewar gwamnan jihar.
Ya kara da cewa, “Yanzu uwar jam’iyya ta yi dukkanin shiri, ta dauko manyan Lauyoyi (SAN) har su hudu wadanda za su je su shigar da wannan kara nan gaba kadan ba da dadewa ba,” A cewar shi.
Gwamnan jihar Bauchi ya kuma yi bayanin cewar magoya bayansu su kwantar da hankalinsu kan wannan matsayar, “A don haka ne nake son na kara muku kwarin guiwa babu inda za a yi daman zalumci ya daure ba, zai iyu ba. Kuma, kowa ma ya sani zaben da aka yi, zalumci aka yi tsokana aka yi, ana son ne nima na yi abun da wasu suka yi, a maida jihar Bauchi baya, wanda yanzu abun da ake son a yi kenan,” Kamar yadda ya ce.
Gwamnan jihar ta Bauchi ya yi zargin cewar daga lokacin da aka sanar da cewar dan takarar jam’iyyar PDP ne ya ci a jihar Bauchi, wai sara-suka ya dawo a jihar, “Ina tabbatar muku daga yanzu zuwa 29 ga watan Mayu nine gwamnan jihar Bauchi; da yardar Allah wadannan tashin-tashina da ake yi ba zan nade hanuna na bari ana wulakanta al’umma ana cin mutuncin al’umma ba. Gobe zan gana da jami’an tsaro za mu yi shiri na musamman yadda za mu yi maganin wadannan aiyukan ta’addanci da ake shirin dawo mana da shi a jiharmu,” Inji M.A Abubakar.
Gwamnan ya tabbatar wa magoya bayansa cewar zai samu nasara, yana mai cewar nasarar tasu ce, ya kuma nuna cewar zai samu nasara a wannan karar da za su shigar.
Da yake maida martani kan jawabin gwamnan jihar, shugaban jam’iyyar PDP a jihar Bauchi Hamza Koshe Akuyam a hirarsa ta wayar tarho da ‘yan jarida, ya shaida cewar suna shirye su tarbi jam’iyyar APC a kotu, ya kuma shaida cewar hakki ne gwamnan jihar Bauchi ya je kotu idan yana da abun da ke nema.
Sai dai ya ce, “Ba kotu ce take baiwa mutum nasara ba, jama’a ne ke zaban mutum har su kaishi ga nasara; su je za mu hadu da su a kotun a shirye muke,” A cewar shi.
Kan zargin dawowar sara-suka da gwamnan ya yi, shugaban jam’iyyar PDP, ya nuna hakan a matsayin farfaganda, yana mai shaida cewar gwamnan Bauchi shine ke da alhakin kare rayukan jama’an jihar, ya ce idan ya tabbatar da akwai masu hakan ya dace ne ya dauki matakin kame duk wanda ya samu da laifin amfani da makami muddin hakan da gaske ne.
LEADERSHIP Ayau, Jumma’a ta nakalto cewar a karin farko dai jam’iyyar APC da gwamnan jihar Bauchi sun je kotun tarayya da ke Abuja inda suke bukaci kotun ta hana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bauchi a karamar hukumar Tafawa Balewa, bayan tafka muhawara kotun ta yi watsi da karar da gwamnan ya shigar gabanta da umurtar INEC ta ci gaba da gudanar da aiyukanta wanda hakan ne ya kai ga sanar da nasarar dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.
Da fari dai gwamnan jihar Bauchi Abubakar ya taya zaabben gwamnan jihar Bauchi murna, ya mika sakon taya murnar ne ta hanun Kakakinsa Ali M. Ali, sai kuma gwamnan ya shaida cewar batun sake zuwa kotun mataki ne da uwar jam’iyyar APC ta dauka, don haka ne ya ce zai mutunta matakin.

Exit mobile version