Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore reshen jihar Bauchi ta ce, daga yanzu duk wani ko wata gidan jaridan da ta sake danganta al’ummar Fulani da ayyukan ta’addanci to za su dauki matakin Shari’a mai tsauri kan kowaye.
A maimakon hakan, kungiyar ta nemi wadanda lamarin ya shafa da su ke ayyana kowani mai laifi da sunansa ba wai ake musu kudin goro ba, “Idan ka ce Fulani ka na maganar kabila ce guda mai dumbin mutane. Don haka duk wanda ya yi laifi sunansa mai laifi ba za mu lamunci kiran Fulani da kalmar ta’addanci ba.”
Wadannan kalamai dai sun fito ne daga bakin Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Bauchi, Alhaji Hussaini Muhammad a yayin wani taron manema labarai da ya kira, ya daura da cewa sakamakon danganta kalmar laifi da ake yawan yi ga al’ummar Fulani, hakan na zubar musu da kima da nuna wa duniya su ta fuska marar kyau.
Ya ce, “Rashin adalci ne muraran ake kiran ‘Harin Fulani Makiyaya’ in fa ka ce Fulani ka na maganar kabila guda ce, an kuma san Fulani a matsayin al’umma masu cikakken dama da hakkin rayuwa bisa dogaro da dokar kasa wanda kuma mu na da hakki a kare mu.
“Makiyayi ya gwanance wajen samar da ci-gaba wa kasa da tabbatar da kyautata kudaden shiga. Yana kiwon domin samar da dabbobin da ake ci da amfana da su.
“Amma da zarar wani ya yi laifi sai a ce ‘Fulani’ alhalin in ka ce hakan ya shafi dukkanin Fulani, don haka ba za mu sake lamuntar hakan ba.
“Ba mu na cewa ba a samu masu laifi a cikinmu ba ne, a’a cewa muke idan mutum ya yi laifi a kashin kansa to a kira sunansa na ‘wane’ a matsayin wanda ya yi laifi kuma hukuntasa daidai da laifinsa.” A cewar Hussaini.
Kautal Hore sai ta nuna damuwarta a bisa abun da ta kira na rashin adalci da wasu jaridu ke musu na kiransu a matsayin masu aikata laifi, “Abun takaici wa mu kawai ake hakan. Yau da za a samu wani dan wata kabila ya kai hari ko ya yi wani aikin ta’addanci, sai ka ga gidajen jaridu su na cewa ‘wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun
kai hari kaza’, ko sun yi fashi ko garkuwa da mutane, amma in an ga da wani kalar Fulani wayyo yanzu za ka ga an jingina wa Fulani.
“Don meye sauran masu aikata laifi ba a kiransu da kabilar da suka fito sai mu? Daga yanzu ba za mu amince da hakan ba, duk wanda ya sake zai fuskaci Shari’a.”
“Abun da muke cewa mai laifi sunansa mai laifi, ba Fulani ba. A kira mai laifi da sunansa kai tsaye,”
“Tarihi ba zan taba mance irin ‘yan ta’adda da aka yi ta kamawa a kasar nan ba, wadanda suka fito daga wasu kabilu na daban, amma ba a kiransu da sunan kabilarsu.
“Don haka mu ma a daina danganta mu da mai laifi, a kira mai laifi da sunansa kawai. Bata mana sunan kabilarmu ya isa haka,” Inji Miyetti Allah.
Daga nan Shugaban kungiyar ya nemi ‘yan jarida da gidan jaridu da suke
musu adalci a rahotonninsu na yau da gobe.