Abba Ibrahim Wada" />

Za Mu Nemi Lashe Kofin Zakarun Turai – Pirlo

Sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Andre Pirlo, ya bayyana cewa zaiyi kokarin ganin kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun turai wanda hakan ba zai kasance ba sai ya kawo canji a kungiyar ta Jubentus bayan da shugabannin kungiyar suka amince su bashi jan ragamar koyar da ‘yan wasan a kakar wasa mai zuwa.
A ranar farkon wannan watan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ta nada tsohon dan wasan ta Andrea Pirlo a matsayin kocinta bayan ta sallami Maurizio Sarri kuma mako daya kenan da nada Pirlo a matsayin kocin kungiyar ta ‘yan kasa da shekara 23.
Zakarun na kasar Italiya sun kori Sarri ne bayan ya yi kakar wasa daya kacal a kungiyar duk da cewa ya lashe gasar Serie A, sai dai an fitar da ita daga Champions League ranar Juma’a tun a zagayen ‘yan kungiyoyi 16.
Wasu rahotanni daga kasar sun ruwaito Pirlo yana cewa zaiyi kokarin ganin ya kawo gyara a kungiyar wadda babu kamarta a kasar ta Italiya kuma zai zauna domin ganin ya karanci matsalolin da kungiyar take fuskanta domin ganin ya cikawa shugabannin kungiyar burinsu na lashe kofin zakaru.
Pirlo mai shekara 41 a duniya ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu har zuwa 2022 sai dai a wata sanarwa da Jubentus ta fitar ta bayyana cewa hukuncin daukaka tsohon tauraron dan wasan Italiya da AC Milan din ya zo ne sakamakon “Pirlo yana da kwarewar da zai iya jan ragama tun daga sanda ya fara buga wasa.
Tuni dai dan wasa Cristiano Ronaldo ya tabbatar da cewa zai ci gaba da zaman kungiyar zuwa kakar wasa ta gaba yayinda kungiyar kuma take fatan sayan dan wasan gaba wanda zai maye gurbin Gonzalo Higuane wanda yake shirin barin kungiyar.

Exit mobile version