Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ne Shugaban Ƙungiyar Izalatil Bid’a Wa’iƙamatus Sunnah (JIBWIS) ta ƙasa. A tattaunawarsa da LEADERSHIP A Yau, ya yi bayanin cigaban aka samu a aikin Hajjin bana, da kuma irin gudunmawar da JIBWIS ta bayar. Har ila yau ya taɓo batutuwan da suka shafi addini da zamantakewa, ga yadda ta kaya.
Akaramakallah ba jimawa kuka dawo daga ƙasar Saudiya inda kuka gudanar da aikin Hajji, a bana ya ka kalli yadda abubuwa suka gudana?
Alhamdulillah! Wasallahu wasallim ala Nabiyyina Muhammad wa alihi wasahbihil waman walahum bi ihsanin ila yaumiddin. Bayan haka Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’alah wabarakaatuhu.
Babu shakka kamar yadda kake magana game da Hajji na bana, kamar ko wace shekara da irin yadda yake zuwa. Na bana ma sai mu ce Alhamdulillahi, an yi aikin Hajji lafiya, Alhazai sun dawo gida lafiya.
Kuma wani abinda zai baka sha’awa shi ne, mafi yawan alhazan Nijeriya da suka yi aikin Hajjin bana manoma ne, wannan ya nuna jama’a sun koma gona, damuna ta yi kyau, kuma an samu amfanin gona mai albarka, tunda har an sayar gashi an zo ibada.
Wannan ya nuna cewa da zamu riƙe noma da kiwo da an fita daga waɗannan wahalhalu da muke ciki, sannan aikin Hajji in kana son ka yi shi ya zama karɓaɓɓe, to sai ka bi malamai sun koya maka irin yadda Manzon Allah ya yi.
Alhamdulillahi malamai sun yi ƙoƙari wajen fahimtar da mutane yadda aiki yake, kuma Hajjin bana ta yi tsari kamar yadda ta saba yi, duk Jihohi mun tura da malamai da za su je su yi wa’azi waɗanda suka samu damar zuwa, dama akwai Kwamiti da hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa ke yi, wanda mai alfarma Sarkin Musulmi shi ya tsara wannan Kwamiti na ƙasa, ita kuma hukumar alhazai tana kula da shi, domin yin haka yana kawo haɗin kai tsakanin malamai.
Amma dai aikin Hajjin bana ba a samu matsala da yawa ba, kuma bayan an sakko daga aikin hajji, mahajjata da mazauna garin Makka sukan ci moriyar zuwan Malamai da suka fito daga Ghana, Nijeriya, Nijar, Burkina Faso, Kamaru, da sauran ƙasashen nan na Afrika. Ta yadda muke tura Malamai suna wa’azi Unguwa-unguwa, Shi ya sa mutanen Saudiya suke cewa suna amfana da Manara TƁ, suna karantuwa da wa’azi fiye da yadda suke ƙaruwa daga Haramin Makka.
Domin dalilin Manara TƁ da wa’azin da malamai suke zuwa daga Nijeriya daga ƙungiyar Izala da haɗin kai da Jami’at ya sa da yawa daga cikinsu sun sauya ɗabi’unsu sun zama mutane kirki, ita kanta gwamnatin ƙasar tana yabawa, kuma an raba mana lasisi da shaidar iznin yin wa‘azi, domin ƙasar ta gane cewa wannan ƙungiya tana karantar da aƙida ne irin wadda ƙasar ke kai.
Muna fatan Allah ya taya mana da fatan hukumomin Nijeriya da hukumomin aikin Hajji za su ƙara ƙaimi, mun san sun yi iya ƙoƙarinsu kuma muna fatan za su ƙara akan ƙoƙarin da suke yi.
Alhamdulillahi babu shakka mun ƙaddamar da wannan gini na masaukin baƙi wanda muka sa wa suna Masaukin baƙin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, don girmamawa, domin shi ne ubammu, shi ya ba mu tarbiyya irin ta addinin musulunci, kuma ya sanya mu akan hanyar gane yadda aƙida ingantacciya take bisa cancanta da gaskiya. Don haka mun girmama gidan, gidaje ne guda huɗu a haɗe wuri guda, ko wanne muka girmama wasu daga cikin manyan malamanmu da kuma shugabanninmu.
Gida na farko muka sa masa Sheikh Marigayi Alhaji Musa Muhammad shugaban ƙungiyar Izala na farko, Allah ya gafarta mashi. Sannan gida na biyu muka sa Sheikh Isma’ila Idris Zakariyya mataimakin shugaban majalisar malamai, shi ma Allah ya gafarta masa, sai gida na uku Sheikh Imam Abubakar Ikara, mataikain Shugaban ƙungiya, shi ma Allah ya gafar ta mashi.
Sai gida na huɗu muka sanya A A Tofa, shi ne Daraktanmu na Agaji, duk waɗannan sun yi wa addaini hidima Allah ya gafart masu, kuma kowane gida ɗaya acikin huɗun nan akwai sunayen waɗannan bayin Allah da suka gabata, ɗungurungun gidan kuma sunansa gidan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Abinda ya bamu sha’awa na yin wannan gida, na farko tukunna, al’ummar musulmi na da buƙatar a samun wani tsaftataccen wani wuri da zai zama masauki ne na baƙi don karramawa, ba za ka samu abinda ya saɓawa addinin musulunci ba.
In ka dubi Otal-Otal ɗinmu masaukan baƙi, zaka ga irin kwamacala da irin abubuwa da ake yi na saɓawa shari’a na da yawa, wanda wasu ma mallakar musulmi ne, kuma muka ga Malamanmu na shigowa nan Abuja, shugabanni na shigowa, sauran al’ummar musulmi Ahlussunnah da muke da alaƙa duk suna shigo wa nan Abuja. Sai muka yi shawara ganin ya kamata ace akwai wani wuri da idan ka zo ba zaka ga wani abu da ya saɓa wa shari’a ba, kamar su giya, ko dai wani abu da bai da fa’ida.
Sai muka lura akwai wata buƙata da ban, to Allah ya taimake mu muna da Manara TƁ mun yi Manara Rediyo, muna da Sunnah TƁ, duk ƙarƙashin wannan ƙungiya ta Jama’atu Izalatil bid’ah Wa’iƙamatus sunnah, lokacin da Allah ya kawo mu wannan jagoranci.
Tashoshin nan tashoshi ne wa’azi, ba yadda za ayi kasa mu Malamin da zai maka wa’azi dole sai ya zo nan cikin Abuja inda wannan gidan TƁ yake.
Wani Malamin zai zo ya yi sati guda, yana ba da gudunmawa a wannan tasha da Malamai da sauran al’umma suke kallo daga ƙasar har Saudi Arabiya, to in suka zo don su yi wannan wa’azi a ina za mu sauke su? Sai Otal, mun yi lissaafin ko wane wata abinda muke kashe wa a ko wane wata jumla sama da naira milyan 1, to sai muka haɗu muka yi shawara cewa, akwai buƙatar mu samu wani wuri da zai zama masaukin baƙi ko ba don jama’a ba ko don kammu, don mu riƙa tattalin waɗannan maƙudan kuɗi da muke kashewa.
To ta yaya za mu gina wannan masaukin baƙi? Muka ce a’ah Allah ya taimake mu muna da wannan tasha tamu ce ta Manara TƁ da Rediyo, muka yi sharara cewa jama’ar Ahulssunnah kowa ya kawo gudunmawa, akwai fatun layya da ake karɓa sadaƙa a tara mana, muka sayar, kuɗin sai muka fara biyan kuɗin (Subsucription) na Manara, da aka samu rara a kuɗin sai muka fara gina masaukin baƙi.
Aka fara wannan abu kamar wasa Allah ya sanya wa abin albarka, Ahlussunah a Nijeriya suka amsa kowa ya ɗauko fatun layyarsa ya kawo saboda Allah, shekara ta farko muka samu kuɗi sama naira Milyan 90, muka ce to Alhamdulillahi, muka sa wani abu ƙaɗan a Manara TƁ sannan muka ce to sai mu sanya ragowar a wannan gini, saboda haka ka ji da yadda aka fara wannan gini.
A shekara ta biyu bara kenan, sai muka sake samun kuɗi naira milya 75, saboda yanayin da aka shiga na rashin tattalin arziƙi aƙasa sai abin ya koma baya, duk da haka muka sake ɗauka muka saka acikin wannan masaukin baƙi.
na musulmai da muka saba yin tafiye-tafiye mun san muhimmancin masaukin baƙi.
Alhamdulillahi mun kammala wannan, kuma a wannan shekarar ma al’ummara musulmi sun sake ba da wannan tallafi da taimako na fatun layya, muka ce to abinda za mu yi nan gaba, shi ne gina Sakateriya ta wannan ƙungiya a nan inda muke, kuma Masallacin da yake cikin Sakateriyar ya yi mana kaɗan, don haka akwai buƙatara sake faɗaɗa.
Har yanzu ba mu kammala karɓar rahoton me muka samu na fatun layyar bana ba, kuma nan ba da daɗewa ba, Kwamitin da Sheikh Yahya ƙaura ke jagoranta za su haɗa alƙaluman da aka samu, kuma ina tabbatar da lallai abin da aka samu ɗin nan bana an samu fiye da abin aka samu bara.
Ya ya batun taimakon nakasassu da wannan ƙungiya take yi musamman guragu da masu hannu ɗaya?
To, da ma ƙungiyarmu ba ta wa’azi kaɗai ba ce, ƙungiya ce da take taimaka wa ɗan Adam, kuma muna taikawa ne da haɗin kan wata Gidauniya mai suna Tolaram dake ƙasar India da muke yi wa guragu ƙafa ta roba, ko wanda bai da hannu.
Kuma duk wanda zai zo a kyauta muke masa wannan aiki, wanda idan asibiti za’a je ayi aikin za’a kashe mafi ƙarancin kuɗi naira dubu 300, kuma mu kan tara mutane aƙalla sama da mutum 500, wani lokaci ma su kan kai mutum 700 zuwa 800, ayi musu aikin nan kyauta, abinda muke yi buƙata a wurin mutum kawai mutum ya kawo kansa nan Abuja daga garinsu
Amma idan ka zo abincinka da masaukinka duk kyauta za mu baka, sannan ƙafar ma a sanya maka kyauta, don ka san wannan ƙungiya tana tausaya maka, saboda wannan abu ka ɗauka Allah ne ya ƙaddara maka, kai kuma ka je ka tausaya wa kanka, ka nemi sana’ar da zaka dogara da kanka kar ka mayar da bara ta zama ita ce sana’arka.
Kuma kamar yadda gwamnati take yin kiraye-kiraye a bar barace-barace, to mu ba da baki kawai mu ke yi ba, irin wannan abu da muke yi ya ƙarfafa wa irin mutanen da muke yi wa gwiwa na tashi tsaye su nemi sana’a.
Domin akwai wani Direba da irin wannan larurar ta rashin ƙafa ta same shi sai ya daina tuƙin, amma da ya zo muka yi masa wannan aiki yanzu ya koma ya ci gaba da tuƙinsa.
Ka ga wannan ba ƙaramar nasara ba ce, don haka muna cikin farin ciki da murna duk wanda ya zo za mu taimaka masa har ma wand aba Musulmi ba, ko yau da muka je akwai waɗanda suka fito daga jihar Bayelsa wata mace ɗaya da ta zo da ƙafa ɗaya kuma ba Musulma ba ce kuma ba ‘yar Arewa ba ce, ta zo nan aka gwada ta aka yi mata duk abinda ya kamata.
Akwai waɗanda suka fito daga Nijar su ma sun zo an yi musu sun koma, don haka daga ko wace jiha daga cikin Jihohin Nijeriya duk an zo Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba, waɗanda ba musulman ba, ba mu cewa sai ɗan Izala kawai, ko ɗan ɗariƙar waye ya zo to za a yi mashi wannan taimako.
Abinda muke cewa kawai waɗanda ba zamu yi wa ba kuma ko yaya, shi ne wanda yake da aƙidar zagin Sahabban Manzon Allah SAW da zagin matan Manzon Allah. Idan ya zo muka gane aƙidarsa kenan, za mu a’a ba yadda za a yi mu taimaki mai zagin Sahabbai ko mai zagin ‘ya’yan Matan Manzon Allah.
Amma wanda ba Musulmi ba ma idan ya zo za mu taimaka masa saboda musulunci ya yarda mu yi mu’amala da ahlul kitabi, kuma ya halatta mana cin abincinsu da aurensu, kuma Allah ya ce suna da addininsu muna da namu.
domin ba yadda za ayi kana kiran kanka Musulmi kuma ka buɗa baki ka la’anci iyalan gidan Manzon Allah SAW ko ka la’anci Sahabban Manzon Allah, har yanzu kuma mu ce muna tare da kai.
Saboda haka waɗannan abubuwa ne na ci gaba muna ƙara godewa Allah Subhanahuu Wata’alah da ya kawo abin a hannunmu don mu tausaya wa al’ummar Musulmi.
Ta wace hanya ake tattaro waɗannan mutane da ake yi wa wannan aiki?
Alhamdulillahi! Muna amfani kafofin yaɗa labarai da na internet wato (Social Media) a wannan ƙungiya tamu, akwaisu a ko wacce Jiha da shugabansu Ibrahim Baba Sulaiman, wanda shi ne jagora idan muna buƙatar bada sanarw, sannan kowa ce jiha wannan shugaba na wannan ƙungiya za a rubuta masa sai a faɗa a Masallaci duk wanda yake da larura iri kaza ya zo a tatance shi, kuma muna bai wa ko wace Jiha (Alocation) na ta kawo mutum ɗari su kuma su rubuta sunansu bayan kwanaki a turo mana, sai mu tura musu ranar da za a yi musu aikin daga nan sai a ɗebo motocin ƙungiya da na haya su zo.
Yanzu dai kaima kana kallo ga waɗansu suna sauka daga wannan ofis, to sun zo ne daga jihar Kebbi, mutanen Gombe ma sun zo, ɗazu mutanen Adamawa sun zo an sallame su, har da ma mutanen zamfara da sauransu.
Duk da kuna Malamai, amma hakan bai hana tofa albarkacin kan abubuwan da suka shafi ci gaba ƙasa ba, wane kira za ka yi game da ɓangaren da suke hanƙoran ganin an raba Nijeriya?
Muna gode wa Allah Subhanahu Wata’alah ya san hikimarsa da ya haɗa mu a Nijeriya, da banbancen addinimu da ƙabilarmu, da yanayin zamantakewarmu.
Domin Nijeriya ƙasa ce da haɗa Ƙabilu daban-daban wand aba wanda zai iya cewa zai zauna shi kadai ba, ko Bahaushe ko Inyamuri, Ko Bayerabe ba wanda zai ce shi kaɗai zai iya zama ba tare da sauran ƙabilun ba.
Masu cewa sai sun ɓalle sai an kasa Nijeriya kashi-kashi Allah ya sani akwai abinda basu dashi mu muna dashi, suma suna da abin da ba mu da shi, ai in baka da wani abu da ni nake dashi kuma muna ƙasa ɗaya dole zaka amfana da shi, haka nima in kana da abin da bani da shi, dole zan amfana da naka.
Saboda haka haƙuri za mu yio da juna bama fatan abin da ya faru a shekaru da suka wuce ya sake faruwa yanzu.
A lokacin da ake ta wannan maganganu cewa nake aci gaba da addu’a Shugabanmu Allah ya dawo dashi lafiya, kuma Allah ya taimake mu shugaba ya dawo gida lafiya, wannan Magana duk sai ta wuce. Saboda kwarjininsa da martabar da Allah ya ba shi.
Muna cikin watan Almuharram, wanda shi ne na farko cikin watanni Musulunci, wane kira Malam yake da shi ga al’ummar Musulmi?
Alhamdulillahi addu’a da muke yi Allah ya sake shigo da mu sabuwar shekarar musuluci Muna addu’ar Allah ya bamu lafiya da za ma lafiya baki ɗaya, a yanzu da yawa daga Musulmi ba su san sabuwar shekara ta kama ba, su dai shekarar da suka sani su ji an ce an shiga watan Disamba, ko kuma su riƙa tambayar yaushe ne watan sha’aban zai ƙare, su ne masu rikici akan ganin watan azumi, su ce su ba za su ɗauki azumi lokacin da aka ce a ɗauka ba.
Saboda haka ya kamata al’ummar Musulmi su gane muhimmancin waɗannan watanni na musulunci su riƙa aiki da su, a riƙa gabatar da ayyuka na alkhairi kamar yawaita sadaƙa karatun alƙr’ani, kyauta da sauran ayyuka na alkhairi.
Wane albishir za a iya yi wa al’ummar Musulmi a wannan shekara da muka shiga?
Alhamdulillahi muna da shirye-shirye da dama, kuma mun mayar da wannan watan wata ne da zamu riƙa yin kasafi na me za mu yi, shi ya sa muka kafa wani Kwamiti a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, Sakatare Janar, dangane da tsare-tsaren da za mu yin a wannan shekara, wannan ‘yan Kwaminti su za su riƙa tantance mana abin da za mu yi a wannan shekara, in Allah ya yarda idan sun kammala za su faɗa mana mu kuma za mu sanya shi ga ‘yan jaridu, kowa ya ga me za mu yi me muke buƙata. Babu ɗaya daga cikin magada na da zai gaji wannan abu, muna yi ne don Allah.
Kuma mun yi kwamiti na zakka da waƙafi, wato yadda ake ba da waƙafi ta yadda mutum zai ce na bada gidana, ko wata kadararsa, duk waɗannan suna daga cikin abubuwan da za mu gabatar, ci gaba gasar karatun ƙur’ani, sannan akwai kacici-kacici bayan gasar karatun da zamu riƙa haɗa makarantu wannan hakan shi zai baiwa ɗalibi tafiya gasar karatun ƙur’ani, ba wai ɗalibi zai yi gaan kansa ba.
Makarantar da za irƙa tantance ɗaliban da za su riƙa fita musabaƙa.
Sannan akwai tsarin wayar da kan jama’a yadda za su fidda zakka da kuma yadda za a tallafa wa marayu, muna fatan wannan kasafi za mu duba mu ga tsarin zuwa wa’azuzzuka da tarurruka da sauran abubuwan da muke yi, sai Makarantu nawa muke da su a Nijeriya, duk cikin wannan shekara muna fata mu gama duk a cikin wannan kasafin an fitar da su.
Sannan mu duba muga yaya za ayi yaranmu su riƙa cin jarrabawa, sai kuma rashin aikin yi da yaranmu suke fama dashi, me ya sa ba a ɗaukar yaranmu aiki? Duk za mu duba irin waɗannan abubuwan, saboda mu ma ‘yan ƙasa ne kuma muna da haƙƙi, ina roƙon Allah ya bai wa shugaban ƙasarmu lafiya, Allah ka bamu lafiya da zama lafiya. Assalamu alaikum.