Daga Zubairu M Lawal, Lafia
Zababben Shugaban kungiyar Hausa Fulani ta jihar Nasarawa Dakta Kabiru Dahiru ya shedawa manema labarai a lokacin da suka zantawa da su a garin Lafia.
Ya ce; wannan kungiyar ba sabon kirkira bane tana nan shekara da shekaru kuma akwai shugabannin da suka tafiyar da ragamar kungiyar na tsawan shekara.
Amma a wannan lokacin sai mukaga cewa ya cancanta a gudanar da zabe domin kara inganta tafiyar kungiyar. Ya ce; da “ni Dakta Kabiru Dahiru da Alhaji NaMairo mubi mukayi takara kuma mebobin kungiyar sun gudanar da zabe Allah yabani nasara Kuma abokin takara na ya tayani murna a wajen, ba tare da nuna damuwar kowa ba. Mun gudanar da komai lafiya .”
Dakta Kabiru ya kara da cewa masu korafi cewa zaben bai inganta ba wadannan basu da hujja saboda su basu shiga zabe ba.
Kuma bai kamata suna dawo da hannun agogo baya ba, idan suna bukatar Shugabanci su shigo a gudanar da komai tare dasu idan lokacin zabe yazo sai su nima idan jama’a sunga cancantarsu su zabe su. Amma yanzu basu da hurumin sukarmu bare su shiga gidan jaridu suna maganganu.
Ya ce ; manufofin da yake dashi na inganta wannan kungiyar shine kokorin tabbatar da hadinkan Ya’yan kungiyar. Da tabbatar da zaman lafiya da wayar da Kansu ta hanyoyin samar da cigaba a duk inda mutum ya samu kansa a kowani gari.
Sannan kungiyar zata samu kusanci da Gwamnati itana a rika damawa da ita a ciki da wajen jihar Nasarawa. Duk wata kungiya idan tana bukatar cigaba to dole ta hada kai ta kuma kusanci Gwamnati komai ayi da ita.
Zamu kara wayar da kan al’umman Hausa Fulani wajen yanka katin zabe da sauransu, saboda mutaninmu a kullun suna zama saniyar ware, duk abinda za a yi suna cire kansu basu shiga a dama da su.