Za Mu Tabbatar Da Ganin Kano Ta Kara Fice A Kasuwanci – Ganduje

Daga Abdullahi Muhammad Sheka

 

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka, cewar zai kara himmatuwa domin Jihar Kano ta ci gaba da rike kambunta na cibiyar ciniki a tsakanin Jihohin kasarnan 36. Kamar yadda Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa Fagge ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.

Gwamnan na wannan bayani ne a ranar Asabar da ta gabata a bikin bajekoli karo 41 da a ka gudanar a filin bajekolin da ke kan titin zuwa gidan adana namun daji da ke Jihar Kano.

Gwamnan wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya wakilta ya bayyana aniyar wannan Gwamnati na rike kambun Jihar Kano da cewa wata ‘yar manuniya ce da ke tabbatar da jajircewar wannan Gwamnati domin jan hankalin masu sha’awar zuba jari daga ciki da wajen kasar.

“Ya na daga cikin kyawawan munufofin wannan Gwamnati sauya kallon da ake wa kasuwanninmu, wanda hakan ne ya fito da hikimar samar da rukunin ‘yan Tebura a Kasuwar kantin kwari wadda ita ce irinta ta farko a fadin arewacin kasarnan,” in ji shi.

Babban alfanun wannan shiri shi ne habaka tattalin arziki da zai taimaka wajen samar da damammaki, samar da ayyukan yi wanda zai habaka samun kudaden shiga, hakan kuma zai rage fatara kwarai da gaske, in ji Ganduje.

Daga nan sai ya bayyana cewa duk da matsanancin ci gaba da fuskantar kalubalen da matsalar rashin tsaro ya haifar, wannan Gwamnati na tabbatar da ganin tsaron rayuka da masu sha’awar zuba jari tare da hadin guiwa da Hukumomin tsaro ne ya sa Jihar Kano ta amsa Jihar da ta fi kowacce zaman lafiya a kasar.

Don haka sai Gwamna Ganduje ya jinjinawa Hukumar Kasuwancin da ciniki (KACCIMA) bisa shirya wannan baje koli, wanda ya bayyana da cewa ya samu ne sakamakon jajircewar mambobin wannan Hukuma domin ganin Jihar Kano ta zama abar koyi a harkar kasuwanci da masana’antu.

Da ya ke gabatar da jawabinsa Ministan harkokin kasuwanci Otunba Adeniyi Adebayo, wanda Alhaji Tukur Muhammad ya wakilta cewa ya yi, taken baje Kolin na wannan Shekarar shi ne, daga darajar masu kananan masana’antu domin cigaban kamfanoni don tafiya daidai da kokarin Gwamnatin tarayya, domin cika burinta na habaka kananan masana’antu, domin tabbatar da ganin abubuwan da su ke sarrafawa sun yi daidai da matsayin kowacce kasa a duniya.

Daga nan sai ya Jinjinawa Kokarin Gwamnatin Jihar Kano da Hukumar Kasuwanci bisa samar da kyakkyawan yanayin gudanar da Kasuwanci duk da kalubalen da tattalin arziki ke fuskanta wanda annobar Korona ta haifar.

A nasa jawabin tunda farko shugaban Hukumar ciniki da Kasuwanci wanda mataimakinsa na daya Jakada Usman Darma ya wakilta ya ce, sama da shekaru nasu yawa mun samu nasarar daga darajar kayan da a ke sarrafawa a cikin gida.

Daga nan sai ya jinjinawa kokarin shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin Jihar Kano bisa habaka harkokin Kasuwanci a kasar.

Exit mobile version