Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Sabon Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, Alhaji Abubakar Zakari (Habu P.A), ya bayar da umarnin janye malaman Gwamnati da ke koyarwa a makarantun da ba na Gwamnati ba a yankin karamar Hukumar Tarauni.
Abubakar Zakari na bayar da umarnin ne a ranar farko da shigarsa ofis a matsayin shugaban karamar hukumar Tarauni dake Jihar Kano, wannan ya biyo bayan samun wadansu rahotanni a lokacin da ya kai ziyarar bazata a sashin ilimin karamar hukumar.
A tattaunawarsa da wakilin mu a Kano, shugaban karamar Hcukumar ya ce, daukar matakin janye malaman makarantar daga makarantu da ake biyan kudi ya zama dole, duba da cewa, malaman da wadancan makarantu ke dauka aro, Gwamnati ke biyansu amma kuma wasu ke amfani da su suna karbar kudade bayan ilimin kyauta ne a Jihar Kano, inji shi.
Da yake karin haske kan janye malaman ba tare da sanarwa ba, shugaban karamar Hukumar cewa ya yi, malaman na Gwamnati ne kuma akwai makarantun ‘ya’yan talakawa da ke bukatar malaman da za su taimaka masu, saboda haka ya zama dole mukiyaye hakkoki da alkawuran da muka dauka na kare hakkin talakawa a kowanne fanni.
Habu P.A wanda ya nuna rashin jin dadinsa da irin wannan hali ya ce, ko kusa Gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci da wasarairai da aiki ba.
Shugaban ya shiga ofis a karon farko tun bayan daukar rantsuwar kama aiki a ranar Juma’ar da ta gabata inda shugaban ya karya da wannan umarni da zai zama kamar tauna tsakuwa ne domin aya taji tsoro.