Za Mu Tallafa Wa Gwamnati Domin Kawar Da Barace –Barace A Kano

An bayyana kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi na yunkurin kawar da barace-barace  ta hanyar  samar da tallafi ga makarantun tsangayu a Jihar Kano, wannan bayani ya fito daga bakin Jagoran Majalisar Mahaddata alkur’ani ta kasa reshen Jihar Kano Gwani Sunusi Abubakar a lokacin da majalisar ta ziyarci kwamishinan ma’aikatar ayyuka da gidaje ta Jihar Kano Honarabul Aminu Aliyu a ofishinsa. Gwani Sunusi Abubakar ya bayyana cewa wannan ziyara ta Mahaddata na da alaka da shirin majalisar na samar da kyakkyawan shugabancin tun daga  matakin kasa, Jiha da Kuma Kananan hukumomi.

Gwani Sanusi Abubakar ya ci gaba da cewa sakamakon taron da majalisar ta gudanar a Kaduna  an amince da samar da hanyoyin da za a rage barace-barace, saboda haka a cewar Gwanin mun kawo wannnan ziyara domin tabbatar da goyon bayan wannan majalisar ga Gwamnatin Jihar musamman bisa wannan aniyarta  na samar da tallafi ga makarantun tsangayu.

Da yake gabatar da na sa jawabin  Kwamishinan ma’aikatar ayyuka da Gidaje ta Jihar Kano Alhaji Aminu Aliyu ya bayyana farin cikinsa da samun wannan babbar majalisa mai albarka, ya ce an kawo wannan ziyara a lokacin da ya dace, musamman ganin Gwamnatin Ganduje Gwamnati ce ta al’umma mai kishin duk wasu al’amurran da suke da alaka da addinin Islama, Hanarabul Aminu Aliyu ya ce ko shakka babu  za mu tabbatar da yin aiki kafada da kafada da wannan kungiya domin ganin an gudu tare an tsira tare, wannan yana cikin abubuwan da Gwamna Ganduje kullum ya kwana ya kuma tashi da shi, hakan ne ma ya sa ake wa Gwamnan lakabi da Khadimul Islam.

A karshe, muna tabbatarwa da wannan majalisa cewa akwai bukatar al’arammomin su fito da duk wasu lakunna domin yi wa wannan Gwamnati addu’ar samun nasarar  da aka a sa a gaba, ya ce lokacin ya yi  da mahaddata alkur’ani  za su fito domin ganin an samar da hanyoyin da za a taimaka wa Gwamnati ganin an kawo karshen wannan matsala ta barace-barace. A karshe ya yi fatan dorewar wannan alaka.

Exit mobile version