Daga Haruna Akaraɗa, Kano
A wata hira da sabon kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Kano, Dr Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi da manema labarai a birnin Kano, ya ci alwashin cewa, za su tantance ’yan siyasar da ke tare da su da kuma waɗanda ke kan Katanga, inda ya nuna takaicinsa kan halayen wasu ’yan siyasa waɗanda uwarsu ba ta mutuwa a siyasa, ya na mai cewa, dole ne nan gaba kaɗan sai kowa ya bayyana ɓangaren da ya ke, domin za su tantance masoyan gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na gaskiya.
Iliyasu Kwankwaso ya ƙara da cewa, wannan lokaci ne na tantancewa, domin manyan siyasar da mu ke da su guda biyu, musamman Arewa ko a jihar Kano ya zama wajibi dole ka bayyana a wane ɓangare ka ke ta hanyar dole sai ka fito ka faɗi ɓangaren da ka ke.
Ya ce, “ba za mu yarda da yaudara ba; ka ce ka na tare da wane, amma ba haka ba ne. Nan da wata shida dole ne sai ka san wa za ka bi, domin siyasa ba a yin ta da dabo. Ba za mu yarda da raba-ƙafa ba. Sai ka faɗi makomarka. Dole mu san da wa za mu gudu tare mu tsira tare.”