Za Mu Yi Aiki Fiye Da Majalisa Ta Takwas- Gbajabiamila

Kakakin majalisar tarayya ta tara, Femi Gbajabiamila a jiya Lahadi ya bayyana cewa; ‘yan Nijeriya su tsammaci kudurori da aiki tukuru daga majalisa ta tara. Gbajabiamila ya bayyana wannan fatan na sa ne a garin Legas a yayin da yake jawabi a taron cin abinci da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar.

Rahotanni sun nuna cewa; taron cin abincin ya samu halartar Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun da gwamnan Filato, Simon Lalong.

Jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Ogun, Segun Osoba, tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajumobi. Sannan gwamnan jihar Legas, Gwamna Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Dk. Obafemi Hamzat, duk suna cikin wadanda suka halarci taron.

Kakakin majalisar ta tara ya ce; duk da majalisa ta takwas ta yi iya bakin kokarinta, amma ‘yan Nijeriya su sanya rai cewa; majalisar ta tara sai ta fi majalisar da ta gabace ta ta fuskokin shimfida ayyuka da kudurori. Ya ce; tabbas ba za su bai wa ‘yan Nijeriya kunya ba. Za su tabbata sun yi wa ‘yan Nijeriya aiki.

Exit mobile version