Daga Sulaiman Ibrahim
Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Oladayo Amao ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Sojojin saman Najeriya (NAF) za su fatattaki ‘yan ta’adda da sauran masu tada kayar- baya a Nijeriya cikin lokaci kadan.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin bikin cin abincin Easter tare da ma’aikatan 013 Quick Response Force Minna, inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da abokan aiki na matukan jirgin pda suka rasa rayukansu a yayin aiki a Allawa a ranar 1 ga Afrilu 2021.
Air Marshal Amao ya sake nanata sadaukarwar shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin saman Najeriya don tabbatar da cewa an kawo karshen masu tayar da kayar baya da ‘yan fashi da makami.
Babban hafsan sojin saman wanda ya samu wakilcin Air Vice-Marshal Remiqius Ekeh ya yaba wa rundunar ta 013 da ke ba da agajin gaggawa da kuma bangaren rundunar GAMA AIKI tare da hafsoshin sojojin sama, yayi kira kuma da su ci gaba da jajircewa wajen yaki da tayar da kayar baya.