Za Mu Yi Wa Boko Haram Bugun Karshe- Buhari

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, nan da ‘yan makwanni masu zuwa ‘yan Nijeriya za su ga yadda gwamnati za ta dauki tsauraran matakan bugun karshe ga mayakan Boko Haram, bugun da shugaban kasar ya ce shi ne bugun karshe na har abada.

A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban kasar ya fitar, Garba Shehu, shugaban ya ce, ya zama dole sojojin kasar su kara azama da nuna bajintarsu ta hanyar fatattakar mayakan Boko Haram baki daya.

Shugaba Buharin ya bayyana cewa; dakarun Sojojin sun cancanci jinjina saboda yadda suka fatattaki ‘yan ta’addan da ke addabar Nijeriya, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafawa sojojin don ganin sun ci gaba da galaba a kan masu tayar da kayar-baya da kawo rashin zaman lafiya a Nijeriya.

Wannan bayanin na shugaban kasar na zuwa ne a bayan harin da Boko Haram suka kai a garin Garkida da ke jihar Adamawa, lamarin da fadar gwamnatin Buhari ta yi tir da shi. Sanann shugaba Buhari ya mika sakon jaje ga iyalan mutanen da harin ya rutsa da su.

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare musamman a yankin arewa maso gabashin kasarnan duk kuwa da cewa a  baya gwamnatin Buhari na ikirarin kakkabe ‘yan ta’addan Boko Haram din.

Exit mobile version